Yau Jumma’a, an gudanar da bikin kaddamar da ginin rumfar kasar Sin a bikin baje kolin hajoji na duniya na Osaka Kansai na kasar Japan na shekarar 2025 a yankin baje kolin na duniya dake Osaka.
Shugaban majalisar bunkasa harkokin cinikayya ta kasa da kasa ta kasar Sin Ren Hongbin, da Wu Jianghao, jakadan kasar Sin a Japan, da babban jami’in gudanarwa na kungiyar baje kolin duniya ta Osaka Kansai ta Japan Hiroyuki Ishige, da gwamnan lardin Osaka na kasar Japan Hirofumi Yoshimura, da kusan wakilai 200 daga sassan gwamnatin Japan da abin ya shafa, da abokan huldar baje koli na duniya, kamfanoni da kafofin watsa labaru sun halarci bikin. Baki daga kasashen Sin da Japan sun aza harsashin ginin rumfar kasar Sin tare. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp