A gun taron manema labarai da aka yi a yau Juma’a, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana cewa, Sin ta lura da rahoton binciken da kungiyar ‘yan kasuwar Amurka dake kasar Sin ta bayar kwanan baya, inda ya nuna cewa, rabin kamfanonin Amurka dake kasar Sin sun mai da Sin wuri mafi dacewa ko wurin dake cikin matsayin koli 3 da za su zuba jari, wanda ya karu da kashi 5% bisa na shekarar 2022. Abin da ya bayyana cewa, kamfanonin ketare dake nan kasar Sin sun amince da makomar tattalin arziki da kasuwarta.
Game da maganar da darektan hukumar leken asiri na kasar Amurka William Burns na cewa, Amurka ta zuba karin kudade da na’urori don tattara da yi bincike kan sirrin kasar Sin da tsayar da shiri dangane da hakan, Wang Wenbin ya ce, Sin za ta ci gaba da kare hakkinta bisa matakan da suka dace.
Yayin da aka tabo maganar hadin kan magance sauyin yanayi, Wang Wenbin ya ce, Sin na fatan hadin kai da kasashen duniya, ciki har da Amurka, da daukar matakai masu dacewa don taka rawar gani wajen tinkarar sauyin yanayi. (Amina Xu)