Mai horar da tawagar ‘yan wasan kasar Afirika, Hugo Bruce, ya bayyana cewar yan wasansa za su canza salon yadda suke taka leda a wasan da za su kara da Nijeriya a ranar Laraba.
Hugo wanda ya tabbatar da cewa Nijeriya ba kanwar lasa bace duba da inda suka fito da kuma yadda suke taka leda da jajircewa a dukkan wasannin da suka buga a gasar AFCON ta bana.
- AFCON 2023: Yadda Abubuwan Mamaki Ke Faruwa A Gasar
- AFCON 2023: Saura Wasanni Biyu Nijeriya Ta Lashe Kofin Nahiyar Afirka
Bayan shafe shekaru 24, kasar Afirika Ta Kudu ta samu nasarar tsallakawa zuwa matakin na kusa da na karshe a gasar AFCON inda za ta hadu da Nijeriya.
A karshe Bruce ya ce duk da ya yarda da yanayin yadda yan wasansa ke taka leda, ba za su dauki karawa da Nijeriya da wasa ba.