Kasar Masar ta sallami babban kocinta Rui Vitoria, bayan da tawagar kwallon kafa ta kasar ta fice daga gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON) kamar yadda hukumar kwallon kafar Masar ta tabbatar a ranar Litinin.
Korar ta Vitoria, ta biyo bayan rashin nasara da Masar ta yi a hannun Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a bugun daga kai sai mai tsaron raga a zagaye na 16, abin da ya kawo cikas ga fatansu na lashe kofin AFCON karo na tara.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta EFA ta fitar, ta godewa Vitoria da mataimakansa saboda hidimar da suka yi amma ta nuna cewa suna nazari domin zabo sabon koci da zai maye gurbin Rui.