Shugaban karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, Abdullahi Garba Ramat, ya yi murabus.
Shugaban wanda aka zaba a watan Maris, 2021 ya yi aiki har zuwa ranar Litinin 5 ga watan Fabrairu lokacin da ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.
- Kun Kasa Magana A Lokacin Buhari, Ba Ku Da Damar Sukar Tinubu – Matasan Arewa
- Cire Tallafin Fetur: Ma’aikatan Jihar Jigawa Sun Ki Amincewa Da Karin Albashin Naira 10,000
Ya ce, “Alhamdullah, yau na damka harkokin karamar hukumar Ungogo ga mataimakina. Na yi iya kokarina wajen tabbatar da daruruwan ayyukan raya ababen more rayuwa kuma na samu lambar yabo da yawa da suka hada da kwararre hazikin shugaban karama da yafi dukkan shugabannin kananan hukumomin jihar da Majalisar Jiha ta ba ni.”
Ramat ya mika ragamar mulkin ne a yayin wani dan karamin biki inda ya kaddamar da tallafawa mata 500 da kuma bayyana tambarin majalisar.
Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan na zuwa ne kwanaki kadan kafin cikar wa’adin shugabannin kananan hukumomin jihar.
A halin yanzu, shugaban karamar hukumar Nassarawa ta Kano, Auwalu Lawan Sha’aibu, wanda aka fi sani da Aranposu, ya koma jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar.
Aranposu wanda dan jam’iyyar APC ne ya bayyana ficewarsa ne a shafinsa na Facebook da safiyar Talata.