Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta kai zagayen karshe na cin kofin Afirka (AFCON), bayan doke kasar Afirka ta Kudu a bugun da ga kai sai mai tsaron gida.
Wannan nasara da Nijeriya ta samu a wasan kusa da na karshe ya samu ne bayan an tashi wasa da 1-1, inda aka kara lokaci na mintin 30, daga bisa aka buga dukan daga kai sa mai tsaron gida.
- AFCON 2023: Za A Kece Raini Tsakanin Nijeriya Da Cote de’Voire A Wasan Karshe Ranar Lahadi
- AFCON 2023: Muna Alfahari Da ‘Yan Wasan Super Eagles -Tinubu
Dukkan bangarorin biyu sun kai wa guna hare-hare, sai dai babu wanda ya samu nasarar zuwa kwallo.
Nijeriya ta zura kwallaye hudu a bugun daga kai sai mai tsaron gida, inda ta zubar da kwallo guda daya, yayin da tawagar ‘yan kwallon Afirka ta Kudu suka zura kwallaye 3 bayan da suka zubar da guda biyu.
Nijeriya dai ta taka rawar gani sakamakon irin kwazon da ta nuna lokacin wannan wasa da tawagar Afirka ta Kudu.