Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, ya bayyana cewa ‘yan bindiga suna wani shiri na kai masa farmaki saboda su nuna cewa ba a samun nasara a sha’anin tsaro.
Gwamnan yana wannan kalanmai ne a wajan taron masu da tsaki akan sha’anin tsaro da gwamnati ta kira domin fuskantar matsalolin da ake fama da su na rashin tsaro a jihar Katsina.
- Jirgin Yakin NAF Ya Kashe ‘Yan Ta’adda, Ya Lalata Maboyarsu A Dajin Katsina
- Gwamnatin Jihar Katsina Za Ta Sake Tsara Ayyukan Hakar Ma’adanai
Haka Dikko Umar Raɗɗa ya ci gaba da cewa ‘yan bindiga sun fito da wani sabon salo na kai farmaki ga jama’a, ya ce yanzu babu masu basu bayanan sirri (Informers) shi ne yasa suke son kai farmaki kan mai uwar da wabi.
‘Ni kai na ina da bayanan sirri da ke nuna cewa ‘yan bindiga suna son kai mun farmaki, amma ni wannan bai dame ni ba, kuma ba zai sa in yi ƙasa a guiwa ba ga abinda muke yi Insha’Allahu zamu ci gaba ‘ in ji shi.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙara da cewa yanzu haka ‘yan bindiga sun gayyato mutane daga wasu jahohi domin su nuna gazawar gwamnatin jihar Katsina na ƙoƙarin da take yi a kan harkokin tsaro.
Haka kuma ya ja kunnen al’umma da su haɗa kan su waje ɗaya domin kare kansu daga hare-haren wuce gona da iri da ‘yan bindiga ke kaiwa jama’a marasa karfi.
Kazalika, ya ƙara da cewa idan ba a ƙara himma wajen ɗaukar matakai ba, to lallai abu ne da zai iya jawo matsalar da ba za a yi fita daga cikin ta ba da sauƙi.