A wannan tattaunawar da aka yi da Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatinsa ta kafa rundunar tsaro na kanta da aka yi wa lakabi da ASKARAWAN ZAMFARA (CPG) domin su taimaka wa jami’an tsaro a yakin da ake yi da ayyukan ‘yan ta’adda da sauran masu laifukka a sassan jihar. Mataimakin Editanmu Bello Hamza ne ya nakalto muku daga jaridar Daily Trust. Ga dai yadda hirar ta kasance.
Menene dalilinku na kafa wannan rundunar tsaron da aka yi wa lakabi da ASKARAWAN ZAMFARA?
Kamar yadda ka sani Jihar Zamafra na fuskantar matsaloli da dama, daga cikin su kuma akwai matsalar tsaro, an yi shekaru a na yaki da mastalar, ta ki ci ta ki cinyewa; saboda haka duk wata gwamnati da ta damu da al’amuran mutanenta dole ta muhimmantar da lamarin tsaro, wannan shi ne babban dalilin da ya sa muka shirya samar da wannan rundunar. Alhamdulillahi sun samu horo na tsawon wata biyu da rabi, an kuma kaddamar da su don su fuskanci yaki da ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, barayin shanu da dukkan nau’o’in ta’addanci a fadin Jihar.
Wannan gwamnatin ta zuba jari mai yawa don kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda da sauran ayyukan bata gari a jihar. Babu wata gwamnati mai mutunci da za ta yi sako-sako da harkokin tsaro.
A halin yanzu mun kaddamar da dakaru 2,645 a zango na farko, muna sa ran daukar dakaru fiye da 5,000, za a ci gaba da daukar ne daki-daki. Za mu auna su muga yadda suke gudanar da aikin su, da kuma irin kalubalen da suke fuskanta, daga na za mu yanke shawarar daukar karin dakarun in akwai bukatar haka. Kamar yadda nace, samar da tsaro na da muhimmanci don kuwa babu wani abin da za a iya yi a jiha dama kasa baki daya in har babu cikakken tsaro.
Mun samar da dukkan abin da ake bukata don samun nasarar dakarun na CPG, tun daga lokacin da aka dauke su aiki da horas da su, don mun tabbatar da aikinsu yana tafiya yadda ya kamata kuma cikin sauki.
Gwamnati ta samar musu da kayan aiki na zamani, tun daga motocin sintiri, kayan sadarwa, mashina don su samu saukin gudanar da aikin a cikin sauki, mun kuma basu alawus-alawus din su tun daga lokacin da aka fara horas da su har zuwa yanzu, za kuma mu ci gaba da basu kudaden su wata-wata. Muna kuma shirin sanya su a cikin tsarin ishora musamman ganin irin hadarin da ke tattare da aikisu. Muna haka ne don karfafa su wajen gudanar da aikinsu.
Yaki da mastalar tsaro na bukatar dabaru da dama, wani mataki za ku dauka bayan kaddamar da Rundunar Askarawan Zamfara?
Lallai haka abin yake, yaki da matsalar tsaro na bukatar dabaru da dama, dole ka fahimci irin matsalar da kake fuskanta. Dole ka fahimci wurin da dake gudanar da yakin ya kuma kamata ka fahimci dalilin da ya samar da irin ta’addacin da kake fuskanta da sauransu.
Wadannan dakarun za su taimaka wa ayyukan jami’an tsaronmu ne irinsu ‘yansanda, sojoji, DSS, sibil defence wajen yaki da ‘yan ta’adda. Muna fatan hada dabaru ne masu yawa amma hakoronmu gaba daya shi ne yaki da ‘yan ta’adda a sassan jihar.
A kan haka ne na ayyana dokar ta baci a banagare biyu masu muhimmanci, sashin ilimi da lafiya. Kamar yadda ka sani in har kana son samun nasara a yaki da ta’addanci dole ka daga darajar rayuwar al’umma saboda hakan zai taimaka wajen rage ayyukan masu aikata laifi a cikin al’umma.
Ina mai tabbatar muku da cewa, a cikin wata shida mai zuwa, da ikon Allah za a ga canje-canje masu muhimmanci a bangarori uku; tsaro, lafiya da ilimi a Jihar Zamfara. Byan wadanna bangarori uku, ana ci gaba da gine-ginen hanyoyi a babban birnin jihar, Gusau, ayyukan sun yi nisa sosai. An fara aikin ne, nan take bayan mun kama aiki, kuma duk da matsalolin shari’a da muka fuskanta ba mu dakatar da aikin ba. Alhamdullilah a halin yanzu babu wani shari’a a wuyan mu, saboda haka al’umma Jihar Zamfara su saurari ayyukan ci gaba daga wannan gwamnatin. Sun zabe mu ne don mu yi musu aiki, kuma za mu yi musu aiki, da yardar Allah ba za mu basu kunya ba.
Rahin Hadin kai da aiki tare shi ne babbar matsalar da ke fuskanta runduunonin tsaronmu, ta yaya zaka tabbatar da hadin kai a tsakanin dakarun Askarawan Zamfara da kuma jami’an staronmu?
Za mu tabbatar da cikakken tattaunawa a tsakaninsu, a halin yanzu ma akwai tattunawa ta musamman a tsakanin dakarun Askarawan Zamra da sauran bangarorin runudunar tsaronmu. Za mu ci gaba da jawo su kusa. Inda kuma muka samu bambanci ko rashin fahimta a tsakaninsu. Za mu tattauna don mu ci gaba. Ina da tabbacin ba za mu samu matsala da jami’an tsaronmu ba.
Kamar yadda na fada, dukkan rundunonin tsaronmu sun bayar da gudummawa wajen kafa dakarun CPG, tun daga daukar dakarun da kuma yadda aka horaasa da su. Inaa da tabbacin dakarun CPG ba za su samu mastala da rundunonin tsaron gwamnatin tarayya ba.
Yana da sauki a kafa irin wannan rundunar, amma babbar matsalar shi ne tabbatar da ci gaban ta. Wani tabbaci zaka ba al’ummar jihar Zamfara na cewa, dakarun CPG sun zo ke nan?
To, da farko dai muna da ciakkiyar kudurin tabbatar da ganin wannan shirin ya samu nasara, kuma abin da ake bukata kenan, a kan haka ina mai tabbatar maka cewa, za mu tabbatar da dorewa tare da wanzuwar dakarun CPG.
Tsaro abu ne mai matukar muhimmanci gare mu, ba za mu yi wasa da shi ba, da yardar Allah za mu samu cimma dalilin kafa rundunar da kuma samun nasara.
Sannan kuma muna da dokar da ta kafa dakarun CPG. Tun da farko sai da muka mika lamarin ga majalisar dokoki inda suka zartar da dokar da ta kafa dakarun CPG. Haka kuma a yayin daukar jami’an mun shigar da sarakunan gargajiya tun daga masu unguwanni, dakatai, hakimai da sarakunan yanka. Mun kuma yi aiki tare da dukkan bangarorin jami’an tsaronmu. Mun yi aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki a kokarin kafa rundunar Askarawan Zamfara, muma kuma da tabbacin za su ji dadin aiki tare da.
Dukkan gwamnonin jihohin arewa sun halarci taron kaddamarwar, me ya mayar da bikin zama na musamman?
Halartar su wani baban lamari ne, zaka iya ganin Gwamnonin Kebbi, Sokoto, Jigawa, Kano, Katsina yayin da mataimakin gwamnan jihar Kaduna ya wakilici jihar Kaduna, wannan yana nuna yadda shugabanin suka muhimmantar da lamarin tsaro.
Mun yi taruka da dama a tsakaninmu inda muka tattauna matsalar tsaron da ke fuskantar arewacin Nijeriya, musamman yankin arewa maso yamma, wannan kuma yana faruwa ne ba tare da banbancin siyasa ba, lokacin harkokin siyasa ya wuce, yanzu lokaci ne na mulkin al’umma, mun kuma damu da halin da al’ummar mu ke ciki, mun damu da halin da arewacin Nijeriya ke ciki, a mtsayinmu na shugabanin dole mu yi wani abu da gaggawa don magance matsalar da al’ummar mu ke ciki. Wannan shi ne dadlilin da ya sa kaga wannan goyon bayan daga dukkan gwamnonin yankin.
Wani sako kake da shi ga dakarun Askarawan Zamfara (CPG) da kuma al’ummar Jihar Zamfara gaba daya?
Ina kira gare su da su tsayu wajen gudanar da ayyukansu. Sun yi rantsuwar gudanar da ayyukansu ba tare da tsoro ko son kai ba, sun kuma yi rantsuwar kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Zamfara, na kuma yi imani da bayanan da suka yi. Na san za su yi abin da ya kamata musamman ganin sun rantse ne da al’ku’ani mai girma, don sun muhimmacin yin haka.
Ina kuma neman ci gaba da goyon baya daga al’umma jihar Zamfara ga wadanna jami’an tsaron namu, saboda samar da tsaro al’amari ne da ya shafi kowa da kowa. Ina kuma rokon su ba dakarun CPG cikakken goyon baya, a kuma ci gaba da addu’ar Allah ya ba mu nasarar cimma burinmu. In muka yi addu’a, tabbas Allah zai amsa mana.