Jam’iyya mai mulki ta APC ta zargi ‘yan adawa daga wasu jam’iyya ne suka haddasa zanga-zanga a Neja da Kano a ranar Litinin kan tsadar rayuwa, domin a taba wannan gwamnati.
A cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na jam’iyyar, Felid Morka ya fitar ranar Talata a Abuja, ya zargi ‘yan adawa da shirya makarkashiya na tunzura mutane su yi zanga-zanga kan tsadar rayuwa wanda hakan zai raunata gwamnati.
- Al’ummar Kano Na Mutuwa Da Yunwa Da Fatara – Gwamna Yusuf
- Tsadar Rayuwa: ‘Yansanda Sun Kama Mutane 25 Da Zargin Yin Zanga-zanga A Minna
A ranar Litinin masu zanga-zanga sun rufe babban hanyar Bida da Kpakungun da ke garin Mina dauke da kwalayen da aka rubuta cewa, “Babu abinci, muna mutuwa saboda yunwa”, “A rage farashin man fetur”, A taimaka mana mu sami abinci cikin sauki.”
Haka zalika, wasu matasa a Jihar Kano sun gudanar da zanga-zanga a kan manyan hanyoyi kan tashin gworon zabi na kayayyakin abinci, musamman ma shinkafa, masara, wake da kuma dawa.
Morka ya bayyana cewa gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu za ta yi duk mai yuwuwa wajen ganin ta kawo sauye-sauye masu muhimmanci da za su taimaka na habaka tattalin arziki da kawo wa ‘yan Nijeriya saukin rayuwa.
Ya gargadi ‘yan Nijeriya su yi watsi da abin da ya kira kokarin tarwatsa kasa da ‘yan adawa ke kokarin yi saboda su cimma burikansu na siyasa.
A cewar mai magana da yawun APC, “Domin nuna yin bore ga gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta, ‘yan adawa sun yi amfani da matasa wurin sudanar da zanga-zanga a wasu manyan burane.
“Zanga-zangar da suka gudana a Neja da Kano shiryayye daga ‘yan adawa, wanda suka yi kokarin tunzura mutane su bujere wa gwamnati saboda tsabar son zuciya. Wannan yunkure ne na tayar da zaune tsaye da barazana ga zaman lafiyar jama’a da kuma kawo rashin tsaro a cikin kasa.
“Yayin da muke ganin hakkin ‘yan kasa ne su yi zanga-zangar lumana, muna kira ga mutanenmu su kasance a ankare kuma ka da su ba da dama ga kokarin da ‘yan adawa suke yi wajen haddasa rikice-rikice.
“Gwamnatin Tinubu ta kafa kwamiti da zai duba hanyoyin sake inganta tattalin arziki da zai taimaka wa ‘yan Nijeriya. Ba tare da hadin kan ‘yan kasa ba wajen yin biyayya ga gwamnati, to shirin ba zai samu ba. A cikin kannanin lokaci, shirin zai sauya alkablar matsin rayuwar da ake ciki a kasar nan.
“Muna kira ga ‘yan Nijeriya da su guji kokarin da ‘yan adawa ke yi na tarwatsa kasa domin samun nasarar siyasa.”