Yayin da wasu yara sune suke taimakawa kansu wajen maida himma wajen karatu yayin da wasu basu da wannan wayon na taimakawa kansu.
Yara wadanda suke suna da saurin gane abubuwan da aka koya masu za su ba da hadin kai a gida, makaranta,da kuma al’ummar da suke tare da su. Rayuwarsu ta kan kasance abar ban sha’awa dan abu kadan za a yi koya masu nan da nan su gane irin hakan kamar basu wani abu hakan yakan basu kwarin gwiwa koda sun fuskanci wani abin da zai daure masu kai dangane da koya masu wani abu da aka yi, alal misali matashin da ake kartfafa ma shi gwiwa wajen ba shi taimako ya kasance kuma yana maida hankali kan abin da aka koya ma shi.
Ga abubuwa wadanda za su taimaka wajen sa idon na tabbatar da yaro yana koyo da gane abin da ya sa gaban shi.
1.Taimakawa wajen bunkasa sha’awar koyo
Saboda a sa shi yaron ya maida hankali kan abin da ake koya masa wato ya kagara bama kamar idan aka lura da alamar yana da sha’awara karatun ko koyon abin da ake kokari da son ya sani. Kamata ya yi duk hanayar da aka san idan an bita za ta taiamaka wajen jan hankalin shi wada ake son ko wadanda ake son, abu mafi dacewa shi ne ayi duk yadda za ayi domin a samu cimma shi burin. Alal misali mai da hankali wajen ganin sai ya kammala wani aikin da aka ba shi a makaranta da kokari na sai cimma nasara wajen samun makin da ya dace. Bugu da kari kuma mahaifi abu mafi da cewa shi ne ya sa ido na tabbatar da shi yaron ko dalibin ya yi shawa’awa kamar yadda za a nuna ma shi yadda za iyi amfani da ilimin shi abin har ya kai. In da aka hadu da matsala wani lokaci shi ne a tsaya tsayin daka har sai an ga yaro ya maida hankalin sa wurin da ake so da ganin zai fi taimakawa rayuwarsa, maimakon shi abin da ake tsammani zai fi ma shi daidai a rayuwarsa.Idan ana matsawa yaro sai ya kammala duk ayyukan da aka ba shi a makaranta, ko ya samu makin daya dace, a irin wannan yanayi ko shakka babu sai shi wanda ake son wawa kan hanya ta gari ya ji dadin abin. Ta wani bangaren kuma idan shi yaron ya gane damuwar shi da ake yi ana son ne a gaba shi ma ya samu nasara shi ma da kan shi zai ba da kai bori ya hau domin shi ma da kan shi yana son ya samu nasarar duk abin da ya sa a gaba. Tunda yake a koyi abu yafi a samu sakamako mai kyau maganar gaskiya sai an amince da al’amarin muhimmancin koyon abubuwan da suka shafi ilimi saboda ai sai an san su kafin ayi tunanin samun sakamakon da zai burge mutane, kamata ya yi a fdadawa yaro ko da shi al’amarin koyo yana da na shi mazaunin na musamman.
2.A rika bada kyauta ta abin da zai ja hankalinsu
Ba yara kyaututtuka ko kyauta duk lokacin da suka yi wani bin bajinta lokacin jarabawa ko a basu wani aikin cikin aji, da dai sauran al’amuran rayuwa na yau da kullun, wani abu ne da za isa su kara maida himma wajen abubuwan da ake koya masu. Abubuwan kyauta kamar sayn lokacin talabishin cake, ice cream, ko wasu kayan wasa suna sa yara su kasance cikin annashuwa kamar dai duk wata kyauta da za a basu ba wata mai tsada ba.Sai dai kuma akwai wadanda suke yi ma wannan al’amari Kallon cin hanci domin an lura da akwai lokacin da aka lura irin wannan maida hankali wajen koyo har a kai ga yin kokarin bazata, abin yana ja da baya ne bama kamar idan aka lura kyautar da aka bada ta dushe.Sannu a hankali su daliban ko matasan suna sabawa da irin halayya ta kyauta da ake ba su da gane muhimmancinta. Yana iya wanke hakoransa ba tare da niyyar yana bukata a bashi wata kyauta ba.Wadannan suna iya bada kwarin gwiwa a wasu wuraren amma kuma ba za su taimaka ba wajen kokrin da ake na cusa wasu halaye na gari.