Gwamnatin kasar Sin ta zartas da wani shiri na gina yankin gwaji na zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta fuskar tattalin arziki da cinikayya a kwanan baya, wanda za a kafa a lardin Hunan dake tsakiyar kasar ta Sin.
Na taba ziyara a lardin Hunan har sau da dama, inda wasu abubuwa guda biyu da na gani suka burge ni. Na farko shi ne, akwai dimbin fasahohin da suke iya taimakawa kasashen Afirka wajen samun ci gaba a lardin, misali fasahar noman sabon nau’in shinkafa da take iya tabbatar da girbi mai armashi, da fasahohin aikin jinya na zamani, da fasahohin samar da motoci masu yin amfani da wutar lantarki da na’urorin masana’antu, da dai sauransu.
- Jirgi Mai Saukar Ungulu Kirar Kasar Sin Ya Kammala Gwajin Tashi Da Sauka A Yanayin Hunturu
- Sin Za Ta Kaddamar Da Gangamin Yayata Ci Gaban Mata
Na biyu shi ne a lardin Hunan ake iya ganin dimbin hadin gwiwar da ake yi tare da kasashen Afirka: Misali a kasuwar Gaoqiao dake birnin Changsha na lardin Hunan, na taba ganin kayayyakin kasashen Afirka iri-iri da ake sayarwa a can, irinsu furannin kasar Kenya, da man kade na kasar Ghana, da dai sauransu. Kana a taron baje kolin tattalin arziki da ciniki na Sin da Afirka da a kan gudanar da shi duk shekaru biyu-biyu a birnin Changsha, na taba hira da ‘yan kasuwan Najeriya, wadanda suka zo birnin don sayen na’urorin aikin gona, kuma na gane ma idanuna yadda aka kulla dimbin yerjeniyoyin hadin gwiwa tsakanin kamfanonin kasar Sin da na kasashen Afirka. Ban da haka, wasu watanni 2 da suka wuce, a garin Zhuzhou na lardin Hunan, na gwada zirga-zirga da wani sabon nau’in jirgi mai suna ART, wanda ya hada fasahohi na jirgin kasa da na motocin bas waje guda. Wannan jirgi na ART ya fi motocin bas iya daukar fasinjoji, kana kudin gina shi ya fi na jirgin kasa araha, saboda haka zai fi biyan bukatun kasuwannin kasashe masu tasowa. Yanzu haka kasar Masar ta riga ta sa hannu kan yarjejeniya, inda take shirin hadin gwiwa tare da kasar Sin don samar da wannan nau’in jirgi a cikin gidanta, kuma tana sa ran samar da jiragen ART ga daukacin kasashen Afirka a nan gaba.
Sai dai a wannan karo, gwamnatin kasar Sin ta kara samar da shirin gina yankin gwaji na zurfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a bangarorin tattalin arziki da ciniki, inda take neman inganta hadin gwiwar Sin da Afirka ta fuskokin zuba jari da ciniki, hadin gwiwar masana’antu, da ta tattalin arziki masu alaka da na’urori masu kwakwalwa na kwamfuta, da cudanya da ake yi a fannin al’adu, da yawon shakatawa, da dai sauransu.
Haka zalika, za a tara fasahohi daga gwajin da ake yi, daga baya a yi amfani da su a hadin gwiwar da daukacin sassan kasar Sin suke yi tare da kasashen Afirka.
Abun tambaya a nan shi ne ko me ya sa ake son gina wannan yankin gwaji a lardin Hunan? Bisa bayanin da Lauren Johnston, masaniyar cibiyar nazarin al’amuran kasa da kasa ta kasar Afirka ta Kudu ta gabatar a cikin rahotannin da ta rubuta, gwamnatin kasar Sin na kokarin gwadawa, da yayata “salon Hunan” da ya shafi hadin gwiwar da ake yi tare da kasashen Afirka, inda take neman daidaita fannonin da ake yawan hadin gwiwa a kai, da karkata daga aikin gina kayayyakin more rayuwa zuwa zuba jari ga kasashen Afirka, da inganta bangaren masana’antun su, da taimakon su a fannonin fitar da kayayyaki zuwa ketare, da samar da karin guraben aikin yi, da raya aikin gona iri na zamani, da fasahohi masu alaka da na’urori masu kwakwalwa na kwamfuta, da dai sauran su. Kana a dukkan fannonin da muka ambata, lardin Hunan na kasar Sin ya riga ya kulla huldar hadin kai mai zurfi tare da kasashen Afirka.
“Salon Hunan” ya nuna cewa, ko da yake kasar Sin ta rike matsayi na abokiyar nahiyar Afirka mafi girma a fannin yawan ciniki cikin wasu shekaru 15 a jere, a daya hannun gwamnatin kasar na ci gaba da kokarin binciken sakamakon da aka samu bisa hadin gwiwa tare da kasashen Afirka a bangaren tattalin arziki da ciniki, da lura da bukatu na kasashen Afirka, sa’an nan ta daidaita tsare-tsaren hadin kan bangarorin Sin da Afirka a kai a kai, don neman samar da karin damammakin haifar da alfanu ga kowa.
A nasu bangare, kafofin yada labarai na kasashen yammacin duniya su kan yi kokarin kara gishiri cikin wasu fannoni masu alaka da hadin kan kasashen Afirka da kasar Sin. Misali, lokacin da kasar Sin ta ba da karin rancen kudi ga kasashen Afirka, sai su ce wai akwai “tarkon bashi”. Kana yayin da kasar Sin ta takaita bashin da take samarwa, su kafofin yada labaran na kasashen yamma su kan ce wai “raguwar tattalin arzikin Sin za ta haifar da matsala ga ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka”. Sa’an nan yayin da kasar Sin ta gina filayen wasannin motsa jiki a kasashen Afirka, sai su ce wai hakan tamkar “salwantar da kudi ne”.
Amma a hakika, idan mun nazarci manufofi na tushe na kasar Sin a fannin hadin gwiwa da kasashen Afirka, za mu ga cewa, tun da can har zuwa yanzu, sun kasance manufar da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar ta nuna gaskiya, da kauna, da sahihanci, gami da samar da hakikanin sakamako, da manufofi na zama cikin daidaito, da amfanar juna, da neman samun ci gaba na bai daya. Wadannan nagartattun manufofi su ne dalilin da ya sa kasar Sin ke neman gwadawa, da yayata “salon Hunan”, da kokarin inganta hadin gwiwarta da kasashen Afirka ta fuskar tattalin arziki da ciniki a kai a kai.
Kana bisa wadannan nagartattun manufofi ne za mu iya sa ran ganin wata makoma mai haske, ta hadin gwiwar da ake yi a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. (Bello Wang)