Dattawan arewa a karkashin kungiyar ‘Arewa New Agenda’ (ANA) sun kimtsa tunkarar gwamnatin tarayya tare da shawarorin kan matakan da za a bi wajen magance matsalolin tsaro da matsin rayuwa, musamman a yankin arewa da ma Nijeriya baki daya.
A cewar dattawan, shawarrarin muddin aka amsa kuma aka yi amfani da su, la-shakka za su kawo karshen matsalolin da suka addabi kasar nan.
- Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Kashe Naira Biliyan Ɗaya Don Aikin Kiwon Lafiya Kyauta Ga Marasa Ƙarfi A Jihar
- Za Mu Daidaita Farashin Abinci Kafin Watan Ramadan – ‘Yan Kasuwar Kano
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Yayale Ahmed, shi ne ya sanar da hakan a lokacin bude taron tattauna hanyoyin yadda za a bi wajen dakile matsalar yunwa a arewacin Nijeriya wanda ya gudana a Abuja a karshen mako.
A Ado Ekiti ta Jihar Ekiti, dattijo kuma babban lauya (SAN), Afe Babalola, ya nemi Shugaban Kasa, Bola Tinubu da ya aiwatar da matakan da za su kai ga kawo karshen matsalar tattalin arziki da tsaro da ‘yan Nijeriya ke fama da su, yana mai cewa matsalolin na matukar ruguza kasar nan.
Shugaban ANA, Ahmad MoAllahyidi, shi ne ya gabatar da shawarorin ga dattawan da suka hada da tsoffin gwamnoni, Isa Yuguda, Sani Yerima, Jonathan Zwingina, Babangida Ngoruje, tsohon shugaban ma’aikata na tarayya, Danladi Kifasi, Fatima Adams da shugaban hukumar alhazai, Jalal Arabi.
Ahmed ya ce, “A matsayinmu na dattawa, mun cimma matsayar gabatar da kanmu domin hidimta wa Nijeriya da kuma ganin mun ciyar da arewacin kasar nan gaba ba wai don mun karaya ba, saboda don mun kasance masu gaskiya.
“Muna son mu canza tsarinmu da dabarunmu wajen magance matsalolin da suka addabi arewacin Nijeriya.
“Nauyin da ke kanmu ba wai kawai mu ce gwamnati ba ta gudanar da aikin da ke kanta ba ne, dole ne gwamnati ta yi aiki tukuru tare da gudunmawa, dole ne gwamnati ta kasance mai daukan dawainiya ta hanyar jajircewarmu.
“Mu kungiyar ‘yan Nijeriya ne masu kishi, sakamakon wannan yunkurin namu za a sanar da jama’an da ke da karfin ikon inganta rayuwar al’umma baki daya.”
Kungiyar ANA ta ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta tallafa wa arewa ta hanyar aiwatar da dokar fara kasuwanci na 2022. A cewarta, wannan kai tsaye zai taimaka wa kamfanonin da suke yankin wajen gudanar da bincike, samar da horaswa da kuma fitar da kayayyaki daidai da yadda ake yinsu a duniyance.
Shugaban ANA ya ce shawarorin za su ba da damar bunkasa harkokin da suka shafi na noma da kuma taimaka wa kowace jiha da ke arewacin Nijeriya.