Tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Muhammad Sanusi, ya ce, a maimakon dora laifin halin kunci da matsatsi rayuwa da ake ciki a Nijeriya ga Shugaban kasa, Bola Tinubu, zarge-zargen da tuhume-tuhumen kai har ma da nuna yatsar, ya kamata ne a yi su kan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kan yadda ya bi wajen janyo matsaloli ga tattalin arziki.
Tsohon sarkin Kano, wanda ke jawabi ta tangaraho a ranar Lahadi a wajen wani taron addini da ya gudana a Abuja, ya ce tsohon gwamnatin da ta gabata ta kasa gudanar da tsare-tsaren da za su taimaka wa tattalin arziki.
- Nijeriya Za Ta Shawo Kan Ƙalubalen Da Take Fuskanta Nan Gaba Kaɗan – Ganduje
- Shugaba Tinubu Ya Gana Da Gwamnoni Kan Ƙalubalen Da Nijeriya Ke Fuskanta
A cewarsa, Buhari ya toshe kunnuwansa kan yadda za a bi wajen magance matsalolin da suka shafi tattalin arzikin kasar nan.
Ya ce, shi kam ba zai biye wa wasu gungun ‘yan Nijeriya da suke son ya soki Shugaban kasa Tinubu kan halin kunci da ake ciki a kasar nan ba.
Sanusi ya ce, “Tsawon shekaru na sha fada kan cewa za a fada matsalolin tattalin arziki. Dukkanin wani masanin tattalin arziki da ya fahimci yadda aka bi da tattalin arzikin kasar nan a shekaru takwas da suka wuce ya san za a iya tsintan kai cikin irin wannan mawuyacin yanayin.
“Wannan kuncin rayuwa da ‘yan Nijeriya ke fuskanta, yanzu ma aka fara shiga muddin ba a dauki matakan da suka dace ba, saboda Nijeriya ba ta kasance wata kasa ta daban ba, irin wannan yanayin ya faru a Jamus, Zimbabwe, Uganda, da Benezuela.
“Tsohon gwamnati ta toshe kunnuwarta ta ki sauraron rokonmu kan matakan da za a bi a kan tsarin tattalin arziki. Na fada a gaban shugaban kasan da ke mulki a yanzu a Jihar Kaduna, cewa duk wani dan siyasan da ya gaya muku cewa abubuwa za su yi sauki, kar ma ku zabeshi, saboda karya yake muku. Mutane sun yi watsi da shawarwarinmu ne da tunanin kawai maganace ake yi ta siyasa.
“Idan zan yi adalci ga Shugaba Bola Tinubu, ba shi ne ya dace a dora wa alhakin matsatsin da ake ciki ba a halin yanzu, sama da shekaru takwas muna rayuwa ciki tsari irin ta karya da lafto basuka daga kasashen waje da ya wuce hankali.
“Ba zan shiga a dama da ni ba wajen sukar Tinubu kan matsatsin rayuwa da ake fuskanta a yanzu ba, ba wai ina cewa shi din ba zai iya yin kuskure ba ne, amma a dai wannan matsatsin da ake ciki, shugaban kasa Tinubu bai da laifi. Zan yi magana muddin na ga wani kuskure a tsarin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu a nan gaba.” Sanusi ya shawarci masu hannu da shuni da su taimaka wa wadanda ba su da shi a halin da ake ciki tare da neman jama’a da su kara hakuri. Sannan, ya shawarci jama’a da su rage buri da dora wa kai abubuwan da ba su wajaba ba domin samun rayuwa cikin sauki da samun abincin da za a ci.