Rundunar hadin gwiwar jami’an tsaron a Yola, sun kama wasu manyan motocin dakon kaya guda biyar makare da siminti da nufin kaishi kasar Kamaru, a garin Jabbi-Lamba, cikin karamar hukumar Girei a jihar Adamawa.
Jami’in yada labaran gwamnan jihar, Humwashi Wonosikou, ya bayyana haka a wani taron manema labarai a hedikwatar ‘yansanda dake Yola, ya nunar da rashin jindadin gwamnatin jihar kan faruwar lamarin, ya ce gwamnatin ba za ta zura ido wasu tsiraru su kawo cikas ga haramcin fitar da kayan ginin ba.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Masallata Uku Da Sace Mutane Da Dama A Katsina
- ‘Yan sanda Sun Kaddamar Da Cibiyar Yin Rijistar Motoci Ta Na’urar Zamani A Kebbi
Ya ci gaba da cewa “Kamar yadda kuka sani, gwamnati ta haramta fitar da kayayyakin gine-gine zuwa kasashen waje domin a rage illar hauhawan farashin kayayyakin.
“Amma abin ya ba mu mamaki da muka samu labarin cewa wasu mutane na ci gaba da yi wa dokar karan tsaye, ta hanyar yin wasu abubuwa na kin bin umarnin gwamnati, duk da cewa an zartar da matakin.
“Don haka gwamnati za ta hukunta wadanda suka aikata laifin rashin bin dokar da aikata wannan aika-aika domin su zama izina” inji Humwashi.
Da shima ke karin bayani jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar SP Suleiman Yahya Nguroje, rundunar ta kafa wata hadakar jami’an tsaro a duk fadin jihar domin tabbatar da dokar kamar yadda gwamnatin jihar ta bukata.
SP Yahya Nguroji, ya ce jami’an tsaron za su raka motocin zuwa wurin da’aka tanadar domin tabbatar da isar da su, kafin kammala bincike.