Adadin sayayyar hajoji ta yanar gizo ta karu, yayin hutun bikin Bazara na kasar Sin da ya kammala. Alkaluman da kamfanonin ba da hidimar biyan kudade na kasar wato “NetsUnion” da “UnionPay” suka fitar a Lahadin nan, sun tabbatar da karuwar sayayyar ta fuskar yawa da darajar kudi.
Kamfanonin biyu sun karbi hidimar biyan kudade ta yanar gizo, wadda yawanta ya kai kimanin biliyan 2.63 a kowace rana, tsakanin ranaikun 9 zuwa 17 ga watan Fabrairun nan, adadin da ya karu da kaso 18.6 bisa dari, idan an kwatanta da na lokacin bikin Bazarar shekarar 2023.
- Durƙushewar Darajar Naira: Atiku Ya Ba Da Mafita Bayan Ya Caccaki Tinubu
- Wang Yi: Sin Ta Sha Alwashin Zama Jigon Samar Da Daidaito A Duniya Mai Tangal-Tangal
Har ila yau, matsakaiciyar darajar hidimar biyan kudade da aka gudanar ta yanar gizo, ta karu da kaso 8 bisa dari idan an kwatanta da makamancin lokaci na shekarar da ta gabata, inda adadin ya kai kudin Sin yuan tiriliyan 1.25, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 176.
Ana alakanta wannan ci gaba ne da bukatun al’umma na lokacin hutu, wanda suka haifar da matukar karuwar hidimar biyan kudade ta yanar gizo, a sassan da suka shafi sayar da abinci, da samar da wuraren kwana, da yawon bude ido, da sayar da daidaikun kayayyaki, da na nishadantarwa. (Saminu Alhassan)