Ƙaramin Ministan Tsaron Nijeriya ya yi tsokaci kan koke-koken da jama’a ke yi kan matsin tattalin arziki da ƴan kasar ke fama da shi a yanzu haka.
Jaridar yanar gizo ta ‘Tarayya’ ta yi karin haske kan cewa, a cikin wannan shekarar, wasu fitattun ƴan Nijeriya, ciki har da Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da shahrarren lauya Femi Falana sun bayyana rashin jin daɗinsu da halin da ƴan ƙasar suke ciki.
- Sace Daliban Zamfara: Matawalle Ya Bayar Da Tabbacin Dawowarsu Cikin Koshin Lafiya
- Gwarzo, Bagudu Da Matawalle Na Cikin Jerin Ministocin Tinubu, Kashi Na Biyu
A makon jiya kuma, ƴan Nijeriya sun yi zanga-zanga a jihohin Neja da Kano da kuma Legas kan matsin rayuwa da suke fuskanta.
Gwamnatin Bola Tinubu ta ce tana ƙoƙarin warware matsalar ta hanyar raba kayan abincin da ke rumbunan gwamnati, sannan ta ɗora laifin taɓarɓarewar tattalin arziki kan tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari.