Karamin Ministan Tsaro, Dokta Bello Matawalle, ya bayar da tabbacin cewa za a kubutar da daliban jami’ar tarayya da aka yi garkuwa da su a Gusau tare da mayar da su gidajensu lafiya.
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da Mista Hope Attari, mukaddashin Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar ya fitar.
- Badakalar Kudade: Kotu Ta Yanke 30 Ga Agusta Don Yanke Hukunci Kan Zargin Da Ake Yi Wa Matawalle
- Matawalle Bai Saci Kudin Jihar Zamfara Ba — Anas Kaura
Ministan wanda ya yi Allah wadai da sace daliban, ya kuma jajanta wa iyaye, malamai da daukacin al’ummar Zamfara kan wannan mummunan lamari.
“Hakika na ji zafi da radadin wannan lamari sosai kuma ina Allah wadai da wannan mummunan aiki da ake zargin ‘yan bindiga aikatawa.
“Don haka ina kira ga jami’an tsaron kasar nan da su sadaukar da kansu da su kara kaimi tare da mayar da hankalin don ganin an dawo da daliban da aka sace.
“Ya zama wajibi dukkanmu mu saka hannayemu mu tashi tsaye wajen ganin an sako daliban da aka sace,” in ji shi
Matawalle ya ce an riga an jibge sassan sojojin sama da na kasa a cikin Zamfara domin daukar kowane mataki na don kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya baki daya.
Ya kuma tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnatin tarayya ta himmatu wajen samar da tsaro ga rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa baki daya.