Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa karya ake masa kan batun cewa ya fice daga APC.
Ya nesanta kansa da wata takardar da aka ce an rubuta daga ofishinsa zuwa ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da yake neman izinin yin murabus daga jam’iyyar APC.
Takardar mai kwanan watan Yuni, ranar 24, shekara ta 2022, mai lamba SH/VP/605/2./0 an nuna cewa, matsin lamba daga iyalai da abokai ne ya sanya Osibanjo fita daga APC.
Babban hadimin mataimakin shugaban kasan a fannin yada labarai, Mista Laolu Akande, da aka bukaci ya tabbatar da takardar da ke yawon, ya misalta ta a matsayin takardar bogi.
A cewarsa turancin da marubucin takardar ma ya yi amfani da shi ba irin salon rubutun Osinbajo ba ne.
Ya ce takardar tana cike da kura-kurai, shi kuma maigidansa ba zai rubuta takarda cike da tarin kuskure ba.
“A ina ma mutane suka samu irin wannan abun? Waye ya ba ku ita? Kodayake, domin kauce wa kokonto da shakku, takardar ta bogi ce. Mataimakin shugaban kasa ba zai taba rubuta irin wannan abun ba,” in ji shi.
Takardar da ke yawon dai mai kanun “Neman Amincewa Don Yi Murabus Daga APC” da aka ce Osinbajo ne ya sanya mata hannu ta ce, Osinbajo ya ce ya yi ganawa daban-daban da iyalai da abokansa inda suka tilasta masa kawai ya fice daga APC. Don haka ne ya nemi izinin Shugaban kasan kan wannan matakin.”
To sai dai Kakakin Osinbajo ya ce duk ta bogi ce takardar.