‘Yan kasuwa a babbar kasuwar sayar da kayan gwari ta Kano, wacce aka fi sani da Kasuwar ‘Yankaba, sun yi kira ga gwamnatin jihar da karamar hukumomar da su inganta kasuwar da sauran kasuwannin jihar.
Sun ce, kasuwannin musamman kasuwar ‘Yankaba na matukar bukatar fadadawa da kuma samar da ababen more rayuwa domin bunkasa harkokinta.
- ‘Ƴan bindiga Sun Kashe Mutum 12 A Kaduna
- Zanga-zangar Tashin Farashin Kayan Abinci Da Matsin Rayuwa Ta Barke A Jihar Oyo
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar, Aminu Lawal, a wata tattaunawa da LEADERSHIP, ya ce, kasuwar ta kara habaka da harkokin ciniki da kashi 80 cikin 100 tun daga lokacin da aka kafa ta a shekarar 1983, inda ya ce, wasu ‘yan kasuwa sun koma amfani da lemomi da gefen hanya don ci gaba da kasuwancinsu.
Lawal ya bayyana rashin sarari, wutar lantarki, ingantattun hanyoyi, haraji mai yawa, matsalar zubar da shara a matsayin manyan kalubalen da ‘yan kasuwar ke fuskanta a kasuwar.
Ya ce, kasuwar tana gudanar da ayyukanta ba dare ba rana, inda ya ce galibin kayayyakin kasuwancin ana sauke su ne da daddare, daga karfe 7:00 na yamma har zuwa safiya, kuma da karfe 5:00 na safe mutane sukan fara tururuwa domin saye da sayarwa.