Mutane a garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, sun fito kan tituna a safiyar yau Litinin don nuna adawa da tsadar kayan abinci da kuma matsin tattalin arziki.
Zanga-zangar, wacce aka gudanar a unguwar Mokola a Ibadan, ta hada matasa dauke da alluna suna nuna rashin jin dadinsu kan yanayin matsin rayuwa da suke fuskanta.
Wasu daga cikin sakonnin da ke jikin allunan nasu sun hada da ‘A kawo karshen hauhawan farashin kayan abinci da farashin kayayyaki,’ da ‘Talakawa na fama da yunwa’ da ‘Tinubu, kar ka manta da alkawuran da ka dauka,’ da dai sauransu wadanda masu zanga-zangar ke dagawa.
‘Yan sanda na tare da masu zanga-zangar a wurin zanga-zangar. jami’an tsaro sun je wurin ne biyo bayan gargadin da rundunar ‘yan sandan jihar ta yi tun farko a ranar Lahadin da ta gabata.