Kungiyar masu gidajen Bahaya a karamar hukumar Bauchi sun kara kudin da suke amsa a wajen masu yin fitsari, ba-haya (bayan gida) da wanka zuwa kaso 100.
Malam Ibrahim Kabo, shugaban kungiyar ne ya sanar da hakan a hirarsa da kamfanin dillacin labarai na kasa a Bauchi ranar Alhamis.
- Gwamna Dikko Umar Ya Taya Kwamarad Dan Ali Murnar Zama Shugaban NUJ Mafi Kwazo A Arewa Maso Yamma.
- Wakilin Sin: Kuri’ar Kin Amincewar Da Amurka Ta Jefa Kan Kudurin Tsagaita Wuta A Gaza Ta Rushe Matsayar Kwamitin Sulhun MDD
A cewarsa, sauyin farashin kudin ya kama naira 200 ga duk mai son yin bahaya a maimakon naira 100 da ake biya a baya, sannan kudin wanka da ruwan zafi ko na sanyi ya tashi daga naida 100 zuwa naira 200.
Kabo ya yi bayanin cewa, dole ce ta sanya su daukan matakin kara kudin zuwa hakan sakamakon yadda kayayyakin da suke amfani da su wajen kula da ban-daki suka yi tsada matuka.
“Muna amfani ne da sabulu, sinadarin wanke bayan gida (detergent), maganin kashe kwayoyin cuta, fetur, man tsaftace hammata ko matse-matsi, bokitaye, tsintsiya, abubuwan zubar da shara, tsunmar share datti (toilet paper) da sauran muhimman abubuwan da muke amfani da su a gidajen wankanmu domin gamsar da jama’a su samu kwanciyar hankalin biyan bukatunsu.
“A gefe guda kuma, mun kara kudin da muke biyan ma’aikatanmu ladar wahalarsu, rawar da suke takawa na da matukar muhimmanci saboda su ne ke kula da tsaftace gidajen Bahaya da kula da su.
“Wadannan dalilan su ne suka haddasa karin kudin zagayawa da na wanka a gidajen Bahaya da suke kwaryar cikin gari,” inji Kabo.
Ya ce a matsayinsu na masu gangamin wayar da kai wajen ganin an dai kashi (tutu) a bainar jama’a, dole ne kuma Mambobin kungiyarsu su kara farashi domin ba su damar iya biyan kudaden da suka dace kuma suka wajaba sannan su cigaba da gudanar da sana’ar ta su.
Da ya ke tofa albarkacin baki kan wannan lamarin, wani kwastoma mai amfani da gidajen ba-haya, Aliyu Danjuma, ya nuna damuwarsa kan karin, amma bai daura wa masu mallakin gidajen ba-haya din laifi ba.