Ikirarin shugabgan hukumar yaki ta cin hanci da rashawa, (EFCC), Ola Olukoyede, ya yi na cewa, akwai wasu manyan ‘yan Nijeriya ne ke daukar nauyin harkokin ‘yan ta’adda a Nijeriya ba wani sabon abu ba ne, ko ba komai bayanin ya tuna wa al’umma ne abin da suka dade suna ji daga bakin manyan ma’aikatan gwamnatin da suka gabata. Abin da ya bambanta a wannan ikirarin shi ne bayanin ya danganta manyan malaman addini da wannan aiki na daukar nauyin ta’addanci a Nijeriya.
Kwanaki ne shugaban hukumar EFCC, Olukoyede ya ce, hukumar ta gano wata kungiyar addini da ke yi wa ‘yan ta’adda safarar kudade da badda da masu da sawun kudadensu. Wannan ya zama wani sabon salo a kan takaddamar da take tattare da bayanan da ake yi a kan masu daukar nauyin ‘yan ta’adda a Nijeriya. Ya kuma kara da cewa, an gano wata kungiyar addini ta na boye wa ‘yan ta’addan kudade, bayan da aka bi diddigin wasu kudade daga ‘yan ta’addan zuwa asusun bankin kungiyar addinin.
- Blinken: Idan Ba Ka Da Karfi, Za A Cinye Ka
- Kasar Sin Za Ta Kafa Tsarin Ba Da Agajin Gaggawa Na Yau Da Kullum Don Inganta Sakamakon Kawar Da Kangin Talauci
“Mun bi diddigin kudaden zuwa asusun kungiyar addinin, da muka bayyana musu abin da muka gano a binciken mu sai muka samu umarni daga sama na mu dakatar da binciken,” in ji shi.
Amma kuma, bayan da rahottanin kafafen watsa labarai ya nuna cewa, bayanan shugaban EFCC na nuni ne ga wata coci, sai gashi sun fitar da wani rahoto mai ban dariya, inda suka ce ba suna nufin wata coci ko masallaci ba ne, amma sunan nufin kungiyar addini ne ko akida.
Sanarwar EFCC ta kuma ce, “Wadanda suke fassara bayanan shugaban EFCC na nuna cewa, yana nufin wata coci ke daukar nauyin ‘yan ta’adda, suna yi ne don cimma wata manufa tasu, wannan kuma ba zai taba kawar da shugaban EFCC daga aikin da ke gabansa ba na tsaftace kasar nan daga harkokin masu yi wa kasa zagon kasa.
Ya kamata hukumar EFCC ta gane cewa, baya ga masu bautar addinin gargajiya da masu sauran addini daban daban akwai kuma manyan addinin kasar nan da suka hada da Kiristanity da addnin musulunci.
Rashin bayyana cikakken sunan coci ko masallacin da ke daukar nauyin harkokin ta’addanci, yanzu kusan makonni ke nan da yin haka, yana nuna lallai kamar hukumar EFCC ta fada dambarwar siyasa ke nan, musamman ganin yau makwanni ke nan da wannan bayanin amma har yau ba mu ji wani matakin da suka dauka ba na bankado kungiyar addnin da suke zargi da daukar nauyin masu aikata ta’addanci ba.
Saboda muhimmanci lamari irin wannan, ya kamata ‘yan Nijeriya su san halin da ake ciki kuma a cikin gaggawa. In har EFCC na so a dauki lamarinta da muhimmanci a nan gaba, dole a cikin gaggawa su sanar da ‘yan Nijeriya kungiyar addinin da ke safarar kudade ga kungiyoyin ‘yan ta’adda tare kuma da tabbatar da an gudanar da cikakken bincike da zai kai ga hukunta duk wanda ke da hannun a kan wannna danyen aikin.
A ‘yan shekarun nan, ‘yan ta’adda sun kashe ‘yan Nijeriya da dama da lalata dukiyoyin al’umma da dama da ba za su misaltu ba. duk da cewa, ba yaki ake yi ba, ayyukan ‘yan ta’adda na tayar da hankula, musamman ganin dimbin al’ummar da suka mutu da kuma wadanda aka raba da gidajensu ga kuma wadanda aka yi garkuwa da su, da kuma miliyoyin kudaden da aka biya da sunan diyya.
A kasar nan, musamman ganin irin tashin hankalin da ke tattare da ayyukan ‘yan ta’addan. Wannan bayani daga hukumar EFCC abu ne da ya kamata a dauka da matukar muhimmanci.
A matsayinmu na gidan jarida, hankalinmu a tashe yake ganin cewa, tun daga lokacin da shugabnan EFCC ya yi wannan bayanin, har yanzu ba a yi komai ba na karin bayani da kuma matakan da za su dauka a kan lamarin, musamman ganin muhimmancin lamarin, muna fatan wannan ma ba zai shude ba kamar yadda wasu lamura masu muhimmanci suke tafiya ba tare da an dauki mataki a kan su ba.
Dalilai da dama sun taikama wajen bunkasar harkokin ‘yan ta’adda a kasar, cikin su kuwa sun hada da rashin tsaro a iyakokin kasar nan, yawaitar makamai a cikin al’umma, talauci da kuma rashin aikin yi a taskanin matasa. Wani abu mai matukar muhimmanci kuma shi ne masu daukar nauyin ‘yan ta’addan, muna kuma kalubalantar jami’an tsaron su bayyana wa al’umma sunaye da adireshin masu daukar nauyin ta’addancin da nufin hukunta su ba tare da bata lokaci ba.
Idan za a iya tunawa gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sha yin magana a kan za ta bayyana sunayen masu daukar nauyin ‘yan ta’adda amma har ya sauka daga mulki bai yi haka ba kuma ba a kai ga hukunta kowa ba. Wannan kuma ya faru ne duk da muhimman bayanai da gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta ba gwamnatin na wadanda suke daukar nauyin ‘yan ta’adda.
A daidai wannan lokacin da kowa da kowa ke bukatar ganin an kawo karshen ta’addanci, dole a yanke kafafen samun kudaden ‘yan ta’adda tare da bayyana sunayen masu yi musu safarar kudaden, ta yadda za su kunyata a idon jama’a, kuma gaggauta gurfanar da su domin hukunta su. Saboda laifin su na daukar nauyin ta’addanci ya fi ayyukan ‘yan ta’addan.