Jami’ar Bayero Kano za ta karrama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da Shugaban Bankin Raya Afirka (AfDB), Dr. Akinwumi Adesina da digirin girmamawa duba da irin gudunmawar da suka bayar a fannin ilimi da ci gaban matasa.
Wata sanarwa da mai ba mataimakin shugaban majalisar dattawa shawara kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya fitar ce ta bayyana hakan a ranar Talata.
- Dalibai 180 Sun Kammala Digiri Da Daraja Ta Daya A Jami’ar Bayero, Kano
- Za Mu Sabonta Dakin Karatu Na Sashen Harsunan Nijeriya Na Jami’ar Bayero — Hassan Baita
Sanarwar ta ce, bikin za a yi shi ne a ranar Asabar, 2 ga watan Maris, 2024 a yayin bukin yaye daliban jami’ar karo na 38 a sabuwar jami’ar da ke kan titin Gwarzo, Kano.
Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya ce, “Hukumar jami’ar ce ta amince da wannan kudirin na karrama su da digirin girmamawa”.