Za a iya cewa kawo yanzu gasar Premier League ta kakar wasa ta 2023 zuwa 2024 ta fara shiga gangara, bayan da aka buga wasannin mako na 25 kuma kungiyoyi uku ne ke takarar lashe kofin bana.
Yanzu saura maki daya tsakanin Manchester City da Liberpool, wadda take jan ragama, kuma saura wasanni 13 a kammala kakar bana kuma a karon farko tun kakar wasa ta 2015 zuwa 2016 lokacin da Arsenal take ta ukun teburi da tazarar maki biyu a kakar da Leicester take ta daya bayan wasa 26, maki biyu ne ke kasancewa tsakanin ‘yan ukun farko.
- Pogba Zai Ɗaukaka Ƙara A Kan Dakatar Da Shi Daga Buga Ƙwallo Na Tsawon Shekaru 4
- Fc Porto Ta Fama Raunin Arsenal A Gasar Zakarun Turai
Karo na bakwai kenan da ba a samun tazara da yawa tsakanin masu fatan lashe Premier League, kuma karo na hudu a wannan karnin wanda hakan yake nuna irin shirin da kungiyoyi suka yi.
Manchester City ta fi wasanni masu zafi da za ta fuskanta nan gaba, wadda za ta karbi bakuncin Manchester United a filin wasa na Etihad daga nan kuma sai ta je gidan Liberpool wato Anfield.
Saura maki daya tsakanin Arsenal da Manchester City, to amma Arsenal tana kan ganiya, wadda ta fara shekarar 2024 da kafar dama, bayan da ta ci wasanni biyar a jere kuma bajintar farko a tarihi da fara shiga shekara.
Za kuma ta ziyarci Manchester City a wasan karshe a gasar mako biyu tsakani idan ta kara da Chelsea a filin wasa Emirates sannan tana da babban wasa da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United a watan Mayu.
Ita kuwa Liberpool wasa daya aka doke ta ranar 4 ga watan Fabrairu a hannun Tottenham a karawa 18 baya, kungiyar da Jurgen Klop ke jan ragama za ta karbi bakuncin Manchester City ranar 10 ga watan Maris, sannan ta kai ziyara Everton mako daya tsakani a wasan hamayya da ake kira Merseyside derby.
Amma dai har yanzu babu wanda zai iya yin hasashen na zahiri da zai iya nuna kungiyar da za ta iya lashe gasar firimiyar Ingila kasancewar duka kungiyoyin suna da wasanni a junansu sannan kuma akwai kungiyoyin da suke biye da su a baya kamar Aston Billa da Tottenham da kuma kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.