An rage hukuncin da aka yanke wa Ebeton kan saba wa dokokin hada-hadar kudi ta gasar Premier daga maki 10 zuwa shida bayan nasarar da kungiyar ta yi a karar da ta daukaka.
An gurfanar da kungiyar a gaban wata hukuma mai zaman kanta a watan Maris bisa zargin tafka laifukan a kakar wasa ta 2021 zuwa 20022, kuma da farko an cire mata maki 10 a watan Nuwamban 2023.
- Pogba Zai Ɗaukaka Ƙara A Kan Dakatar Da Shi Daga Buga Ƙwallo Na Tsawon Shekaru 4
- Liverpool Ta Lashe Kofin Carabao Karo Na 10 Bayan Doke Chelsea A Wembley
Ragin da aka yi kan hukuncin zai sa Everton ta kasance da maki 25 sannan ta koma mataki na 15 a teburin Premier bayan wata sanarwa da hukumar tafiyar da gasar Premier League ta fitar inda ta bayyana cewa “Hukumar daukaka kara mai zaman kanta ta yanke cewa hukuncin da Everton FC za ta fuskanta kan keta ka’idojin kasuwanci na Premier League na kakar 2021 zuwa 2022, zai zama cire mata maki shida nan take.
Hukumar ta ce wannan ya biyo bayan daukaka karar da Everton ta yi na hukuncin da wata hukuma mai zaman kanta ta yanke a watan Nuwamba 2023 na cire maki 10 saboda keta dokokin.
Sanarwar ta kara da cewa wannan hukuncin da aka sake wa fasali zai fara aiki ne nan take kuma za a sabunta teburin Premier daga lokacin da aka yi hukuncin domin yin la’akari da hakan.
Hukuncin farko da aka yanke wanda shi ne mafi girma a tarihin gasar Premier – ya sa Everton ta rikito daga mataki na 14 zuwa 19 a kan teburi amma kuma duk da haka kungiyar ba ta karaya ba, ta dage wajen samun nasara a wasanni.
Har Yanzu Everton da Nottingham Forrest Ba Su Da Makoma Amma kuma har yanzu kungiyoyin kwallon kafa na Everton da Nottingham Forest ba za su iya sanin makomarsu ba har sai bayan kammala gasar Premier ta bana saboda bincike da ake ci gaba da yi.
Everton na murnar rage hukuncin da aka yanke mata daga maki 10 zuwa maki shida bayan ta daukaka kara amma duk da haka Everton da Forrest na da sabbin tuhume-tuhume da ake yi masu sakamakon keta dokokin hada-hadar kudi na gasar Premier League, inda za a gurfanar da kungiyoyin biyu a gaban wani kwamiti mai zaman kansa a farkon watan Maris, kuma dole ne su tabbatar da hukunci kafin ranar 8 ga Afrilu.
Idan har an yanke hukuncin cire maki, kungiyoyin biyu na da kwanaki bakwai domin daukaka kara, sannan dole ne a tabbatar da sakamakon wannan lamari kafin babban taron gasar Premier League wanda za a gudanar a ranar 24 ga watan Mayu, kwana biyar bayan an kammala kakar wasa ta bana.
Hakan na nufin cewa idan har kugiyoyin biyu sun fuskanci hukuncin cire maki suna iya samun kansu a matakin gasar ‘Championship’ ko da kuwa sun kai labari sakamakon wasannin da suka buga a kakar wasa ta bana.