Bankin Raya Afirka (AfDB) ya bai wa Gwamnatin Jihar Gombe tabbacin himmatuwarsa wajen goyon bayan kudurinta na ci gaban jihar, musamman shirinta kan sarrafa amfanin gona (SAPZ) da kuma shirye-shiryen tallafa wa jama’a na (ISDLEIP).
Babban Daraktan Bankin AfDB na Nijeriya, Mista Lamin Barrow ne ya yi wannan alkawari yayin da ya karbi bakuncin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a ofishin bankin da ke Abuja.
- An Halaka Mutane A Chadi Bayan Yunkurin Kashe Shugaban Kotun Koli
- Sassan Ma’aikatun Gwamnatin Kasar Sin Sun Gudanar Da Shawarwari 12,480 A Shekarar 2023
Barrow ya jaddada kudurin bankin na tallafa wa yunkurin Gwamna Inuwa na inganta rayuwar al’ummar Jihar Gombe ta hanyar samar da karin damammaki ga talakawa da marasa galihu ta fuskar samar musu da ababen more rayuwa kamar ruwa, da inganta tsaftar muhalli, da lafiya da ilimi, tare da farfado da sana’o’i da karfafa samar da wadataccen abinci da inganta lafiyar jama’a bisa manufofin shirin na IBSDLEIP.
Ya ce da madatsun ruwa guda ukun da Gombe ke da su, da kasancewarta a kyakkyawan bigire da zaman lafiya da kuma kyakkyawan jagoranci na hangen nesa irin na Gwamna Inuwa, jihar tana kan kyakkyawar turbar samun daukaka da ci gaba.
Da yake jawabi tun da farko, Gwamna Inuwa ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin gwamnatinsa da cibiyoyi irin su AfDB a yunkurin gwamnatinsa na mayar da harkar noma sana’a mai inganci da za ta samar da albarkatu ga kasuwannin gida da na waje.