Assalamu Alaikum Warahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu. Jama’a barkanku da kasancewa tare da wannan fili mai al’barka wanda yake kara tunatar damu abubuwan da muka manta ko muke bukatar kara sani akai.
A wannan makon zan yi magana ne game da abin da ke ci mun tuwo a kwarya wanda ya shafi matasa wato samari da ‘yan mata har ma da iyaye, musamman ta bangaren daya shafi karya/fafa irin wadda samari ke yi wa ‘yan matan da za su aura.
Idan muka yi duba da wannan lokacin da muke ciki za mu ga yadda al’amura ke kara tabarbarewa ta yadda samari ke taka rawar gani wajen sace zuciyar yarinya ta hanyar yaudararta da abin duniyar da ba za su iya ci gaba da samar mata da shi ba bayan an yi aure.
Yayin da su ma iyaye ke taka rawarsu wajen ganin sun kasa nunuwa yaransu gaskiya game da abubuwan da suke gani wanda ya fi karfin hankali da kuma tunani wanda samari ke yi wa yaransu, musamman wajen kashewa yaransu kudin da bai kamata su kashe musu kafin aure ba.
Yayin da su ma yaran/’Yan Mata, ke da nasu laifin na rashin wofintar da duk abubuwan da za su gani wanda yake ba daidai ba ga sanarin nasu, musamman yadda za su rinka kashe musu kudi ba bisa ka’ida ba.
Duk da cewa ba duka ne aka taru aka zama daya ba, ta bangaren samarin da ‘yan mata da kuma iyaye, sai dai a wannan zamanin akwai mafi yawa masu aikata hakan dan burge ‘yan mata da sace musu zuciya, bayan kuma an yi aure yarinya ta shiga cikin gidan sai ido ya raina fata.
Misali; Saurayi ne ya ke son yarinya kuma har zuciyarsa aurenta yake son yi, wala’alla ya kai kudi, kodai bai kai kudin ba, ko an saka rana, ko ba a saka ba, ba mamaki akwai ‘competition’ tsakaninsa da wani, dan yana zargin wani yana sonta yana son ya aureta, sai ya fara kokarin yadda zai durkusar da daya saurayin da yake sonta, ta hanyar saka mata katin wayar da ko shi ba zai iya sakawa kansa ba.
A duk lokacin da yarinyar ta kira shi cewar; ba tada kati ko kuma suna waya katin ya karya sai ya saka mata katin N2000 ko kuma N2500 ko sama da haka, madadin ya saka mata daidai samunsa/daidai aljihunsa.
Sai dai wani hanzari ba gudu ba, abin da samarin ke mantawa da shi har kullum shi ne; A duk lokacin da ka auri yarinya ba lallai ne ka saka mata katin N2000 tare da 10gb din da ka saba saka mata a lokacin da take waje ba, haka kuma dubban kudadan da ka saba zuwa ka kashe mata lokacin bikin kawarta, ba lallai ne duk ka iya yi mata su bayan aure ba.
Da yawan halayya ko tarbiyya irin ta wasu matan shi ne; duk abin da ka saba yi wa mace kafin aure, tunaninta idan ka aure ta za ka yi mata fiye da abin da ka saba yi mata na kyautatawa, misali; ka saba saka mata katin N2000 tunaninta za ka koma na N5000 da zarar an yi aure, kana yanka mata rago idan ka aure ta tunaninta bujimin Sa za ka yanka mata, ka ga kenan hakan ya zama kamar yaudara, kuma hakan ba shi ne zai taimaka wajen zamantakewar auren ba.
Wannan abun na daya daga cikin abin da yake wargaza aure, wanda su kansu iyaye da suke zaune a cikin gida ya kamata su kula da kyau, a duk lokacin da suka ga ‘yarinyarsu koda yaushe wayarta da kudi in tana waya bata kakkautawa ko suka tsinci ‘yarsu da waya mai tsada toh ya kamata su buncika, idan wanda zai aureta ne ya siya mata wannan wayar ko ya ke zuba mata wannan kudin toh ya kamata su kiraho shi, su zaunar da shi, su nuna masa cewa; su ba wannan suke kallo ba, kyautatawar tana da dadi, amma idan ya auretan zai iya yi mata wannan hidimar?
Dan haka ina bada shawara baki daya saurayin da budurwar da ita kanta uwar yarinyar saboda shi uba wani lokacinma bai san halin da ake ciki ba, saboda fita yake ba zama ya ke yi ba, ba komai yake sani ba.
Ke kanki idan saurayi yana miki haka gara ki zauna da shi ki fahimtar da shi, in har so ki ke ki yi aure ki zauna da mijinki lafiya,”wane abun da ka ke mun yayi yawa gara ka rinka tarawa a hankali, in na zo gidan ma amfana”.
Kai ma da ka ke yi bai kamata ba, ka fadawa wacce za ka aura gaskiya, ba maganar boye-boye, ba maganar ka yaudari yarinya da kati ko da kudin kashewa da dai sauransu, sai an yi aure shekara guda ka ji aure ya balle ko an fara samun hargitsi, kati ya koma na dari biyu ko kuma a koma yi wa juna ‘flashing’, wannan kuskure ne babba kuma gaba ce da muke samun matsala, shiyasa za a ga auren baya karko baya zuwa ko ina, saboda ka sabawa yarinya da abubuwan da kai ka san in ka aureta ba za ka ci gaba da hakan ba,
Sau da dama idan aka kai ga wannan gabar su matan ba sa iya hakuri, yarinya za ta ga cewa; ya saba yi mata kowanne irin abu na kudi a waje, sai bayan ta zo gidan ya mallaketa sannan ya daina, ashe yaudara ce?
Magana ta gaskiya wannan shawara ce, ku tsaya ku auna ku gani, irin wannan abun idan ba Allah ne ya rike al’amarin ba, za a ga yarinya ya saba mata da wannan abun, ita fa sai ta samu wanda zai iya yi mata fiye da wannan a zaman auren, sai a ga yarinya karama tana ta yaho a ce aurenta biyu ko uku, toh gaskiya da yarinyar da shi saurayin da su iyayen yarinyar ku tsaya ku yi wa tufakar hanci indai da gaske auren za a yi, to a yi shi bisa sunnar ma’aiki.