Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA, ta ce rumbun ajiyar abinci da aka wawashe a Abuja a ranar Lahadi ba mallakinta ba ne.
Da Safiyar ranar Lahadi, giajen jaridu da dama sun rahoto cewa, wasu matasa da ake zargin bata gari ne sun afka wani rumbun ajije abinci da ake kyautata zaton mallakar hukumar NEMA ne da ke unguwar Gwagwa a babban birnin tarayya Abuja domin kwashe kayan abinci saboda tsadar rayuwa da tabarbarewar tattalin arzikin da al’ummar kasar ke ciki.
- Ban Fara Rubutu Don Daukaka Ko Neman Shahara Ba – Maimuna Tijjani
- Tarihin Hadejia Da Sarakunanta (4)
Wasu mazauna unguwar sun bayyana cewa, matasan sun afka cikin rumbun ajiyar ne da misalin karfe 7 na safe, inda suka yi awon gaba da buhunan masara da sauran kayayyakin abinci.
Sai dai, a cikin wata sanarwa da jami’in hulda jama’a na NEMA, Ezekiel Manzo ya fitar, ya karyata rahoton cewa, rumbun mallakin hukumar ne.