Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris ya raba sabbin motoci kirar Toyota Fortuner Jeep guda 24 ga ‘yan majalisar dokokin jihar, domin kara karfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.
Gwamnan wanda ya mika motocin ga kakakin majalisar Hon. Muhammad Usman Ankwai tare da wasu ’yan majalisa a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi, ya bukace su da su yi amfani da motocin ta hanyar da ya kamata.
- Dubai Ba Ta Dage Haramcin Bai Wa ‘Yan Nijeriya Biza Ba – Fadar Shugaban Kasa
- Yadda Aka Fara Zaben Fidda Gwani A Amurka
Ya kuma lura cewa motocin za su taimaka matuka wajen taimaka wa ‘yan majalisar wajen gudanar da ayyukansu na majalisa da himma domin ci gaban jihar.
Ya yaba da kyakkyawar alakar aiki da ke tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa, wanda a cewarsa, ya samar da hanyar gudanar da ayyukan raya jihar daban-daban cikin sauki, wadanda ke da alaka kai tsaye ga rayuwar jama’a.
Gwamna Idris ya karfafa gwiwar ‘yan majalisar da su dore da kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da jihar domin samun ci gaba cikin sauri da ciyar da jihar a gaba.
“Dole ne na bayyana a nan cewa ina jin dadin zaman lafiya da ke tsakaninmu, ban taba samun sabani da shugaban majalisar ko da mambobinsa ba.
“Wannan, a zahiri ya taimaka mana wajen aiwatar da ayyuka a duk masarautunmu na gargajiya da muke da a fadin jihar don amfanin mutanenmu,” in ji shi.
Gwamnan ya tuna cewa ya saya tare da raba sabbin motoci guda 30 ga jami’an tsaro, 28 ga kwamishinoni da wasu shugabannin hukumomin.
Ya ce: “A yau muna shaidar rabon sabbin motoci kirar Toyoa Fortuner Jeep guda 24 ga ‘yan majalisar dokokin Jihar Kebbi.
Ya ce gwamnatinsa ta zabi sabbin motoci ne domin kaucewa duk wata gazawa wajen gudanar da ayyukansu.
Daga nan sai ya bukaci wadanda suka ci gajiyar motocin da su yi amfani da ababen hawan domin cimma manufar da aka nufa da su.