Hukumar kula da yanayi ta kasa (NiMet), ta yi hasashe tare da nuna damuwa kan yanayin da za a shiga nan gaba a yanayi zafi.
Sauyin yanayi wanda ya hada da zafi, sanyi da kuma samun ruwan sama suna tasiri sosai ga barkewar cututtuka.
- An Kama ‘Yan Sintiri 10 Kan Zargin Kashe Limamin Garin Mada
- Boko Haram Ta Kone Gidajen Da Aka Gina Wa ’Yan Gudun Hijira A Borno
Cututtukan sun hada zazzabin cizon sauro, sankarau da kuma wasu cuttutuka da suke da alaka da yanayin sauyin yanayin.
Cibiyar Bincike ta Duniya da Yanayi ta Al’umma (IRI), ta bayyana cewa yanayi zafi zai kai kashi 80 da kuma matsakaicin zafin jiki zuwa kashi 18 da 32 da yanayin zafi sama da sama da kashi 60 su suke taimakawa wajen kyankyashe kwayoyin halittar cutar.
Hukumar ta ce a watan Janairun 2024 yanayin zai iya bai wa kwayoyin halittar sauro damar zuba kwayayensa da kuma samun damar kyankyashe su, wanda hakan ne ke taimakawa wajen yada cutar.
Hukumar ta ce irin wannan yanayin shi ne ake tunani da kuma hasashen cewa zai faru a wasu daga cikin yankunan Nijeriya.
Hukumar ta jaddada cewa sauyin yanayi da ake samu wanda yake sauyawa ba tare da daukar lokaci ba.
Don haka, da zarar wadannan yanayi sun daidaita, akwai yiwuwar kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro.
Ana sa ran zuwa watan Afrilu, hukumar ta yi hasashen yiwuwar kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro a jihohin kudancin kasar nan, wanda ya bambanta da kananan da ma wasu yankuna.
Haka zalika, hukumar ta yi hasashen irin wannan yanayin a watan Maris, inda ta ce akwai yiwuwar cutar zazzabin cizon sauro a jihohin Sakkwato da Katsina da Zamfara da kuma Jihar Kano.
Sauran jihohin sun hada da Jigawa da Bauchi da Yobe da Borno.
Sannan hukumar ta kuma bayar da shawara ga yankunan Kebbi da Neja da Zamfara da Kaduna da Taraba da Adamawa da Filato da Benuwe da Kwara da Kogi da Nasarawa da kuma babban birnin tarayya Abuja, su kanasance cikin shiri.