Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce an kama akalla ‘yan banga 10 kan zargin kashe wani malami a Jihar Zamfara.
A ranar Talata ne aka yi wa Sheikh Abubakar Hassan kisan gilla, inda ake zargin ‘yan banga da hannu a lamarin da ya faru a Karamar Hukumar Gusau.
- Jakadun Kasa Da Kasa Dake Sin: Kuzarin Tattalin Arzikin Sin Zai Amfani Kasashen Duniya
- Xi Jinping Ya Gana Da Wasu Membobin Majalisar CPPCC
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa wadanda ake zargin ’yan sintiri ne ba ‘yan-sa kai a Jihar da aka tura kwanan nan ba ne.
“Gwamnatin Jihar Zamfara ta samu labarin kisan gillar da aka yi wa Sheikh Abubakar Hassan Mada a garin Mada, abin bakin ciki ne, sosai kuma fatan kar hakan ya sake faruwa.
“Jami’an tsaro sun kama dukkan ‘yan sintiri da ake zargi da hannu kan wannan danyen aikin, muna so mu bayyana cewa ‘yan sintiri da ake zargi da hannu a kisan ba su da alaka da ‘yan-sa kan Jihar Zamfara.” kamar yadda ya bayyana a cikin sanarwar.
Gwamnatin ta ce sakamakon binciken farko da ‘yansanda suka gudanar ya nuna cewa daya daga cikin wanda aka kama tsohon dalibin malamin ne da aka kashe.
Bayanin zai taimaka wa hukumomi su fahimci lamarin da kuma daukar matakan da suka dace.
A cewar gwamnati, za ta gabatar da sakamakon binciken da ‘yan sanda suka gudanar da zarar an kammala shi.
Ta kuma aike da sakon ta’aziyya ga iyalan malamin da jama’ar garin Mada.