Sanin kowa ne cewa Nijeriya na cikin tarnakin fatara da yunwa. Ba kowa ba ne ya ke iya ciyar da kan sa da iyalin sa, ballantana ya gudanar da wasu harkokin na rayuwa.
Akwai ma masu cewa Nijeriya ta fi kowace kasa fama da fatara a duniya. Duk da yake hakan ba gaskiya ba ne, amma yanayin da ake ciki ya sanya tilas shugabanni su fito da hanyoyin rage halin kunci da ake fama da shi.
A daidai lokacin da gwamnatin Buhari ta zo, duniya gaba daya ta auka cikin halin karayar tattalin arziki saboda faduwar farashin man fetur. A cikin 2016 kasar ta fada cikin ramin karayar tattalin arziki wanda ba ta taba ganin irin sa ba a tsawon shekaru 25. Masana sun ce tattalin arzikin mu ya tsuke da kashi 1.6 cikin dari inda kashi 43 cikin dari na jama’ar kasar (wanda ya kama mutum miliyan 89) su ke rayuwa cikin matsanancin talauci, sannan wasu kashi 25 cikin dari (mutum miliyan 53) su ke gab da fadawa cikin irin wannan mugun yanayin.
Ko a wannan shekarar ta 2022, Bankin Duniya ya fitar da wani rahoto inda ya ce yawan ‘yan Nijeriya masu fama da fatara zai karu zuwa mutum miliyan 95.1 a bana kadai. A rahoton, mai taken ‘Don Inganta Rayuwar Dukkan ‘Yan Nijeriya: Nazari kan Fatara a Nijeriya a Cikin 2022’ (a turance, ‘A Better Future for All Nigerians: 2022 Nigeria Poberty Assessment’), rahoton ya nuna yadda faruwar annobar korona (COBID-19) ya kara ta’azzara yanayin fatara da yunwa a Nijeriya, ta yadda an samu karin mutane miliyan 5 da su ka auka cikin kangin fatara.
Rahoton ya ce saboda karyewar tattalin arzikin kasashen duniya baki daya, ko da a ce annobar korona din ba ta zo ba, za a samu karin matalauta daga mutum miliyan 82.9 a shekarar 2018/19 zuwa miliyan 85.2 a shekarar 2020 da miliyan 90 a cikin 2022, musamman saboda karuwar yawan jama’a da ake samu.
To amma kuma saboda faruwar annobar sai ya kasance fatara ta karu daga kashi 40.1 cikin dari a cikin 2018/19 zuwa kashi 42.0 cikin dari a 2020 da kuma kashi 42.6 cikin dari a 2022, wanda hakan ya nuna cewa matalauta miliyan 89.0 ake da su a cikin 2020 kuma za su karu zuwa miliyan 95.1 a cikin 2022. Don haka, annobar ita kadai ta tura karin ‘yan Nijeriya miliyan 3.8 cikin fatara a cikin 2020, da karin mutum miliyan 5.1 da ke cikin fatara a cikin 2022.
Bankin Duniya, wanda ya kunshi masana harkar tattalin arziki, ya bada shawarar cewa lallai ne gwamnati ta fito da hanyoyin rage matsin fatara da ke damun mutane masu karamin karfi. An shawarce ta da ta fito da wasu tsare-tsare da za su taimaki talaka, musamman wajen samar da aikin yi da taimaka wa manoma da ma ayyukan gida da ba su shafi noma ba, da samar da kayan more rayuwa irin su wutar lantarki da hanyoyin sufuri.
Bankin ya kara da cewa lallai ne gwamnati ta samar da yarda da aminci a tsakanin ta da wadanda ta ke yi wa mulki, kuma ta aiwatar da shirye-shirye wadanda mutane za su gani a kas har su yarda da su.
A bisa irin wadannan shawarwari, tun a cikin 2016 gwamnatin Buhari ta fito da Shirye-Shiryen Inganta Rayuwa na Kasa, wato ‘National Social Inbestment Programmes’ (NSIP), wanda wani gungun tsare-tsare ne da aka kirkira don nemo tushen fatara da ke tofo a kasar nan a sare shi. Wadannan muhimman shirye-shirye an dora alhakin aiwatar da su ne a wuyan sabuwar Ma’aikatar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya.
Tsare-tsaren wannan shiri na NSIP su na da yawa (irin su N-Power da bada tallafi ga matan karkara). Daya daga cikin su shi ne Shirin Ciyar Da ‘Yan Makaranta, wato a turance ‘National Home Grown School Feeding Programme’ (NHSFG). A karkashin wannan tsarin, an rika ciyar da daliban makarantun firamare na gwamnati ‘yan aji 1 zuwa aji 3 a kullum, wato daga Litinin zuwa Juma’a. A kan kashe N70 wajen bai wa yaro abincin rana.
Abin mamaki shi ne, duk da irin alfanun da ke tattare da shirin (wanda za mu yi maganar su nan gaba kadan), sai ya kasance wasu ‘yan Nijeriya su na sukar sa, su na cewa ba su ga amfanin sa ba.
Na ga suka kala-kala musamman a makon jiya lokacin da ma’aikatar ta bayyana karin kudin abincin kowane yaro daga N70 zuwa N100. Kanun labaran da jaridu su ka buga, wato za a kashe naira miliyan 999 wajen ciyar da ‘yan makaranta a kowace rana, ya dauke hankalin jama’a, har wasu na cewa, “Kawai an fito da sabuwar hanyar sata!” Wasu kuma sun ce maimakon wannan shirin ciyarwar, a karkatar da kudin zuwa ga wani shirin na daban.
Da yawa masu sukar shirin sun kalli yawan kudin da aka ce za a rika kashewa ne, ba tare da la’akari da yawan daliban da za a ciyar ba, wato yaro miliyan 10 a kowace rana. Haka kuma da yawa ba su fahimci shirin ba ballantana su gane alfanun sa. Wasu kuma tsantsar adawa ce kadai ke cin su.
Kamar yadda na fada, wannan shiri wani bangare ne na babban shirin rage radadin fatara a Nijeriya, wato ba shi kadai ba ne, domin akwai wasu wadanda Ma’aikatar Jinkai ke aiwatarwa. Dukkan wadannan tsare-tsare su na cimma nasara, kuma ba za ka gane hakan sosai ba har sai ka tattauna da wanda ya ke cin moriyar su.
Babbar manufar fito da shirin ciyar da ‘yan makarantar firamare ‘yan aji 1 zuwa 3 shi ne a karfafa wa iyaye matalauta su rika barin ‘ya’yan su su je makaranta. Iyaye da dama ba su iya daukar nauyin kai ‘ya’yan su makaranta, musamman idan ba su iya ba su kudin abinci da ake kira “kudin tara” wanda yara ke ci a makaranta. Dauke masu wannan nauyin ba karamin sauki ba ne a gare su.
Su kan su yaran, wani yaron ko don ya samu wannan abincin mai dadi zai iya sanya shi ya rika dokin zuwa makarantar, ya zauna a ciki har ya yi karatun. Yanzu ma da aka ce za a rika bada kwai ga kowane yaro a duk ranar Laraba, abincin nasu ya kara armashi.
Idan kai ka fi karfin irin wannan abincin, kila ba za ka fahimta ba. Amma ka tambayi wadanda abin ya shafa, ka ji yadda su ke ji a ran su.
A bara, gwamnatin Jihar Kano ta bayyana irin alfanun da ke tattare da shirin ciyar da daliban. Kwamishinan Ilimi na jihar, Alhaji Muhammad Salisu Kiru, ya ce shirin ya haifar da karuwar shigar da yara makarantar firamare ‘yan aji 1 zuwa 3 daga yara miliyan 1.2 zuwa miliyan 2.9.
Ya ce musamman ya kafa wani kwamiti wanda ya tabbatar da wannan karin da aka samu. Ya ce, “Na san yara na da tunani sosai idan sun ji ana bada abinci kyauta za su so su rika zuwa makaranta domin koyon karatu.” Ya kara da cewa gwamnatin Jihar Kano na karbar naira biliyan 1.5 a duk wata daga hannun Gwamnatin Tarayya.
A da fa kenan, lokacin da N70 ake kashewa wajen ciyar da kowane yaro. Yanzu saboda tsadar rayuwa da tashin farashin kayan abinci, aka ga tilas ne a kara kudin da N30, wato ya koma N100. Shin ko a hakan ma, ina ne za ka je ka ci abincin N100 ka koshi? Masu cewa ana kashe kudi ba kan-gado sun manta da hauhawar farashin da kayan abinci ke yi ne. Ko waye aka ce ya ciyar da yaro da N100, har ya dan samu riba a matsayin sa na dan kwangila, zai yi kukan cewa kudin sun yi kadan. Ga shi kuma Bankin Duniya ya ce fatara za ta karu a bana; gobara daga kogi kenan, maganin ta Allah!
Sannan masu cewa kashe naira miliyan 999 a rana daya kudin ya yi yawa, ba su yi la’akari da yawan daliban ba ne. Daliban firamare a duk fadin Nijeriya fa aka ce, kuma dalibai miliyan goma. To kai mai suka idan kai ne, nawa za ka kashe?
Wani abu da mutane ba su gane ba shi ne ba fa Minista Sadiya ba ce za ta kashe kudin ko kuma ma’aikatar ta ce za ta rika kashe kudin. Rashin sanin haka ya sa wasu na zargin cewa wai ministar za ta wawure kudin ne kawai.
Amma a yadda ake gudanar da tsarin, ita Ma’aikatar Jinkai aikin ta shi ne ta rarraba kudin ga gwamnatocin jihohi, su ne za su aiwatar da aikin ciyarwar, domin fa daliban firamaren duk nasu ne, ba na Gwamnatin Tarayya ba; su ne su ka san daliban nasu da inda su ke.
Kuma ko su gwamnatocin jihohin, ba su ba ne za su kashe kudin kai-tsaye ta hanyar bada kwangilar dafa abinci da raba shi a makarantu. Akwai kwamiti a ko wace jiha da ya dunshi jami’an gwamnatin jihar da na tarayya, da kuma wakilan kungiyoyi masu zaman kan su da sauran su.
’Yan wannan kwamitin, su na zaune a jiha, su na jiran isowar kudin daga Gwamnatin Tarayya. Da ma sun gama shirin su tsaf: sun tantance daliban da makarantun da ‘yan kwangilar. Don haka da zaran kudi ya zo, sai aiki kawai. Saboda haka, kamar yadda babu ruwan minista da wannan kudi, to shi ma gwamna ba ruwan sa. Haka kuma babu ruwan wani kwamishina ko hedimastan firamare da wannan kudi. Kudi ne da ba su ciwuwa irin yadda wasu mutane su ke tunani.
Wani babban alfanun wannan shirin shi ne yadda ya yi naso a cikin tsarin tattalin arzikin kasa. A nan, ina nufin yadda mutane iri daban-daban za su amfana da shirin ta fuskar aikin da za su yi wa shirin. Na farko, an dauki ma’aikatan shirin, an rage masu zaman kashe wando; na biyu, an dauki mata masu girka abinci aiki. Ga ‘yan kwangila masu sawo kayan abincin. Manoma ma za su amfana domin za a rika sayen kayan da su ka noma a cikin daraja, ana kaiwa makarantu domin girkawa.
Ka dauki masu kiwon kaji, a karamin misali. A kowace Laraba, za a raba kwai guda miliyan 10 ga dalibai duk a fadin Nijeriya. Don tabbatar da ingancin kwan da kuma tsare gaskiya wajen sayen sa, za a rika sayen kwan ne ta hanyar ‘ya’yan Kungiyar Makiyaya Kaji ta Nijeriya (Poultry Association of Nigeria). Wadannan kwai miliyan 10 da za a saya a duk mako daya, ba karamar taimaka wa makiyayan kaji zai yi ba; lallai aljifan su za su yi nauyi!
Ko ta ina dai idan ka kalli wannan tsarin, za ka ga cewa nagge dadi goma ne, domin ya na wanzar da alfanu ba guda daya kacal ba. Zai taimaka wajen rage radadin fatara, ba ga iyaye da dalibai kadai ba, har ma ga manoma da masu dafa abinci da mahauta da ‘yan kwangila da masu jigila da mota da sauran su. Karfafa hanyoyin tattalin arzikin jama’a ya na daga cikin manufofin tsarin. Ganin tasirin sa a rayuwar jama’a ne ma ya sa Bankin Duniya ya yaba da shi, ya ke tallafa masa da shawarwari da kayan aiki da kudi. Idan har mutum ya kafe a kan cewa bai ga amfanin shirin ba, to ko dai adawa ke damun sa ko kuma bai ilmantu kan manufar shirin ba.
A sabon garambawul din da aka yi wa shirin kwanan nan ke aka kudiri aniyar kara kudin ciyar da dalibi daga N70 zuwa N100. Kuma ba Ma’aikatar Harkokin Jinkai kadai ce ta zauna ta yanke hukuncin hakan ba, sai da ta zauna da wakilan masu ruwa da tsaki a tsarin, wato irin su da Shirin Abinci na Majalisar dinkin Duniya (World Food Programme), da Hukumar kididdiga ta kasa (National Bureau of Statistics), da Hukumar Fadakarwa ta kasa (National Orientation Agency, NOA), da kungiyar Inganta Abinci ta Duniya (Global Alliance for Improbed Nutrition, GAIN), da Ma’aikatar Aikin Gona ta Tarayya da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, da ma wasu. Saboda haka, wannan shiri ne wanda kowa ya dace ya yi na’am da shi don dimbin alfanun sa ga jama’ar Nijeriya.
Ibrahim Sheme dan jarida ne mazaunin Abuja