Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) ta yi gargadin cewa yakin da ake yi a Sudan zai iya janyo fitinar yunwa mafi tsanani a duniya, muddin ba a kawo karshensa ba.
Fiye da wata 10 kenan ana gabza fada tsakanin bangarori biyu da ba sa ga maciji da juna, lamarin da ya kai ga mutuwar kimanin mutane 14,000.
- Sojojin Nijeriya Sun Yi Nasarar Fatattakar ‘Yan Ta’adda A Katsina
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Daliban Tsangaya 15 A Sakkwato
Haka kuma rikicin ya raba mutane miliyan takwas da muhallansu kuma mafiya yawan al’ummar kasar ba a san me suke ciki ba, ga kuma, karuwar yunwa.
Yayin da ake ci-gaba da fada, yawancin iyalai na ci-gaba da tserewa zuwa kasashen da ke makwaftaka.
Inda su kan isa sansanoni ba tare da komai ba, cikin ja’ibar yunwa suna masu matukar bukatar taimako.
Yayin wata ziyarar da ta kai wani sansani da ke Sudan ta Kudu, Shugabar Hukumar Abinci ta Duniya, Cindy McCain, ta ce an manta da mutanen da yakin ya shafa.
Ta ce akwai bukatar a bai wa hukumomin agaji damar kai wa ga wadanda rikicin ya kebance don taimaka wa wadanda yunwa ta addaba.