Sojojin Nijeriya sun kai farmaki a hanyar Maikusa da ya kai su ga samun nasarar kashe babban kwamandan ‘yan ta’addan da Modi Modi ke jagoranta a Jihar Katsina. Wannan farmakin da aka aiwatar a Kananan Hukumomin Kurfi da Safana, ya nuna irin jajircewar da sojoji ke yi na kawar da ta’addanci a yankin.
A yayin wannan kazamar arangamar, sojojin sun fuskanci turjiya daga ‘yan bidigar amma duk haka, sun nuna bajinta, inda suka yi galaba akan su da karfi ta hanyar sakin wuta babu sassautawa.
- Mahara Sun Sace Dalibai 200 A Kauyen Kaduna
- Hukumomin Sauraron Korafe-Korafen Jama’a Na Kasar Sin Sun Lashi Takobin Samar Da Muhallin Kasuwanci Mai Kiyaye Doka
Sakamakon wannan nasara da aka samu ya kai ga kashe Maikusa da wasu ’yan ta’adda uku, wanda hakan ya nuna muhimmin ci gaba da ake samu na yunkurin kakkabe sansanonin ‘yan ta’addan.
A ci gaba da musayar wutar, sojojin sun kwato manyan makamai da suka hada da bindigu kirar AK-47 guda biyu, da kwanson harsashi, da harsashin 65 mm 7.62 mm, bindigar kirar a gida, da kakin soji mai rod-rodi. Wannan gagarumin aiki na nuni da irin tasirin da sojoji ke da shi wajen wargaza hanyoyin sadarwar ta’addanci.
Yunkurin da sojojin suka yi na kawar da ‘yan ta’addar ya kara bayyana ne yayin da sojoji suka kara fadada ayyukansu, inda suka lalata sansanonin ‘yan ta’addan a kauyukan Wurma, Shaiskawa, Yauni, Dogon Marke (Larmar Kurfi), da kuma kauyukan Ummadau da Zakka (Karamar Hukumar Safana).
Wannan cikakken tsari na nufin kawar da ragowar gungun ‘yan ta’adda, tare da tabbatar da dorewar tsaro da tsaro a yankin.
Rundunar sojin Nijeriya na ci gaba da kai farmaki a yankin gaba daya, inda ta nuna aniyar ta na kare yankin da kuma kawar da duk wata barazana. Wannan gagarumar nasarar na nuna jajircewar da sojoji ke yi wajen yaki da ta’addanci, wanda ke nuna wani gagarumin ci gaba na samun dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Katsina.