Yau da karfe 3 na yamma, an gudanar da bikin rufe taro na biyu na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ko NPC karo na 14. Babban sakatare na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin kolin soja, Xi Jinping, da sauran shugabannin jam’iyyar da na kasa sun shiga wurin taron don halartar bikin rufe taron.
A wajen rufe taron, ‘yan majalisar dokokin kasar Sin suka zartas da kuduri kan rahoton aikin gwamnati, kazalika, sun zartas da dokar da aka yi wa kwaskwarima ta majalisar gudanarwar kasar, ta kuma amince da shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekarar 2024, da amincewa da babban kasafin kudin shekarar 2024, har ila yau, sun zartas da kuduri kan rahoton aiki na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama ‘ar kasar Sin (NPC), da zartas da kuduri kan rahoton ayyukan kotun kolin jama’ar kasar, da kuduri kan rahoton majalisar masu shigar da kararrakin jama’a na kasar. (Safiyah Ma, Yahaya)