Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ta cafke wasu mutane hudu da ake zargi da aikata damfara a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dele Oyewale ya fitar ranar Litinin a Abuja.
- Ramadan: ‘Yansandan Kano Sun Buƙaci Jama’a Da Su Ba Jami’an Tsaro Haɗin-kai
- Wane Lokaci Ne Ya Kamata Mu Yi Kwalliya Da Azumi?
Oyewale ya ce ana zargin mutane hudun da aike da sanarwar karbar bashi ta bogi ga wasu mutane a Maiduguri.
Ya ce jami’an EFCC sun kama wadanda ake zargin ne a ranar Juma’a a cikin babban birnin Maiduguri, bayan samun bayanan ayyukan damfara da suka yi.
“Bincikenfarko ya nuna cewa wadanda ake zargin suna yin damfara ne ta hanyar amfani da manhajar kasuwancin wani banki wajen siyan abinci da abubuwan da ba na abinci ba tare da karbar kudi daga masu sana’ar POS, ta hanyar tura musu kudin bogi.
“Za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike,” in ji shi.