A jiya Litinin ne mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing, ya jaddada bukatar mambobin Kwamitin Sulhu na MDD, su tsaya tsayin daka kan ruhin hadin gwiwa.
Wannan kira ya zo a lokaci mafi muhimmanci la’akari da yanayin da duniya ke ciki. Babban makasudin MDD shi ne dinke baraka da tabbatar da hadin kan kasa da kasa bisa adalci da girmama juna. Haka kuma batun yake ga duk wasu sassa dake karkashin majalisar, ciki har da Kwamitin Sulhu, wanda nauyin tabbatar da sulhu da tsaro a kasa da kasa ya rataya a wuyansa.
- Salon Dimokuradiyya Mai Sigar Musamman Ta Kasar Sin
- Xi Ya Tattauna Harkokin Kasa Tare Da Wakilai Da Mambobin Manyan Taruka Biyu Na Kasar Sin
Batun zaman lafiya da tsaro bai kamata ya zama wani abu da za a siyasantar ba, domin ya shafi rayuka da dukiyoyin jama’a. Ya kamata tabbatar da tsaron rayukan jama’a ya kasance wani abu da ya sha gaban komai, haka kuma, bai kamata a rika amfani da shi a matsayin makami ba.
Yanayin da duniya ta shigha yanzu haka, inda ake fuskantar rigin-ginmu, ya dace ya zaburar da kasashen duniya cewa, ana tsananin bukatar hadin gwiwa da kira da murya daya domin kare rayukan jama’a da tabbatar da kwanciyar hankalin duniya.
Kamar yadda Jakadan na Sin ya bayyana, gabatar da daftari, nauyi ne maimakon wata dama. Nauyi ne da ya rataya a kan kasashen na tabbatar da sun yi abun da ya dace cikin adalci da hangen nesa da sanin ya kamata, ba wai amfani da shi a matsayin dama ta siyasa ba. Ran bil adama, abu ne mai daraja, bai kyautu a rika sanya siyasa cikin duk wata harka da ta shafi ceton rai ko rayuka ba. Yadda ake amfani kujerar dindin din a matsayin dama ko kuma makamin siyasa a MDD, ya kara ta’azzara lamuran a duniya, maimakon tsagaita bude wuta da cimma sulhu, ana ta zubar da jini da asarar rayuka da dukiyoyi.
Kamar yadda kasar Sin take kira a kullum, tabbatar da zaman lafiya a duniya na bukatar hadin gwiwa da cudanyar bangarori daban-daban. Bugu da kari, kamata ya yi kasa da kasa, musammam manya su yi koyi tare da amincewa da wannan ra’ayi na kasar Sin, wato ra’ayin tabbatar da adalci da zaman lafiya da hadin gwiwa da kuma tsayawa kasashe masu tasowa da goya musu baya. (Fa’iza Mustapha)