A ranar 5 ga watan Maris ne aka bude taron shekara shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin a birnin Beijing, babban birnin kasar ta Sin, kuma wakilai kimani 3000 daga wurare da kabilu da sana’o’i daban-daban ne suke halartar taron, don sauke nauyin dake wuyansu bisa tsarin mulki da dokoki. Majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta kasance hukumar koli ta kasar, kuma a gun taronta na shekara shekara, a kan tattauna da kuma yanke shawara kan manyan manufofi da dokoki da nada jami’ai.
Long Xianwen: Babban nauyin da ke bisa wuyana shi ne in jagoranci mazauna kauyenmu don tabbatar da samun ci gaba da wadatar kauyen.
- Masani Dan Najeriya Na Dora Muhimmanci Kan Raya Sabon Karfin Samar Da Hajoji Da Hidimomi Masu Karko Da Sin Ke Yi
- Damben Boxing: Anthony Joshua Ya Doke Francis Ngannou A Saudi Arabia
“Babban nauyin da ke bisa wuyana shi ne in jagoranci mazauna kauyenmu don tabbatar da samun ci gaba da wadatar kauyen”, furucin malam Long Xianwen ke nan dan majalisar wakilan jama’ar kasar Sin.
Long Xianwen ya fito ne daga kauyen Niujiaoshan da ke gundumar Guzhang na yammacin lardin Hunan na kasar Sin, inda ‘yan kabilar Miao ke rayuwa. Yau shekaru sama da 10 da suka wuce, kauyen ya kasance cikin talauci, inda matsakaicin kudin shigar da mazaunansa suke samu a shekara bai kai kudin Sin yuan 800 kwatankwacin dala 115 ba. Har ma akwai wakar da ‘yan kabilar Miao kan rera a wurin da ke cewa, “kada mata su auri mazan kauyen Niujiaoshan, inda ake fama da talauci, kuma daga cikin maza 10, 9 sun kasance gwauraye.”
Amma yanzu kauyen ya samu matukar gyaran fuska, inda a karkashin jagorancin Long Xianwen, mazauna kauyen suka yi amfani da albarkatun da suke da su, suka fara noman bishiyoyin ganyen shayi a duwatsu, baya ga bunkasa harkokin yawon shakatawa, matakin da ya sa cikin shekaru sama da 10, aka fitar da kauyen daga kangin talauci, inda matsakaicin kudin shigar mazaunansa ya karu da sau 18. A matsayinsa na jagoran kauyen, Long Xianwen ma ya samu goyon baya sosai daga mazauna kauyen. Tun daga shekarar 2018, sau biyu a jere ne aka zabe shi a matsayin dan majalisar wakilan jama’ar kasar Sin. A game da batun, Long Xianwen ya ce, “Ina mai godiya game da aminci da aka ba ni, wallahi zan yi kokarin in kara samar da gudummawa ga kauyenmu.”
A matsayinsa na dan majalisar, Long Xianwen kusan ya tafi kowane sashe na karkarar yankin yammacin lardin Hunan, kuma ta hanyar ziyartar al’umma da kamfanoni da hukumomi da sauraron ra’ayoyinsu da gudanar da bincike, ya fahimci ainihin matsalolin da suke fuskanta, tare da bayyana ra’ayoyi da ma shawarwarinsu a wajen taron majalisar wakilan jama’ar kasar, ta yadda gwamnatin kasar za ta samu damar fahimtar matsalolin da al’ummarta ke fuskanta tare da daukar matakan warware su.
“A matsayina na dan majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, wanda na fito daga yankin karkara, ya zama dole in fahimci matsalolin da sassan karkara ke fuskanta wadanda ake matukar bukatar a warware su.” Don haka, ya mai da hankali sosai a kan bunkasuwar ayyukan jigilar kayayyaki a yankunan karkara, da inganta aikin samar da hidimomin al’adu ga jama’ar yankunan da sauransu. A yayin da yake kan kujerar dan majalisar, ya gabatar da shawarwari sama da 20, wadanda akasarinsu suka samo tushe daga binciken da ya gudanar a yankunan karkara da ke yammacin lardin Hunan.
A shekarar 2022, ya gabatar da shawarar gina madatsar ruwa ta Xujialing a gundumar Guzhang, a kokarin inganta aikin noman ganyayen shayi a gundumar. Ya ce, “Na ziyarci sassan noman ganyen shayi da dama a gundumar Guzhang, inda na gano cewa, duk da ci gaban da aka samu wajen noman ganyen shayi, amma sakamakon yadda sassa da dama ke kan tuddai, sun fuskanci matsalar samun ruwa daga kusa, matsalar da ta yi wa bunkasuwar aikin noman shayi na wurin tarnaki.
Shawarar ta samu goyon baya daga sassan gwamnati na matakai daban daban, har ma gwamnatin kasar Sin ta sanya shi cikin kasafin kudinta don tallafa wa aikin gina madatsar ruwan. Bisa ga shirin, madatsar ruwan za ta kai ga ban ruwa ga gandun noman shayi da gonaki da dazuzzuka na yankuna bakwai da ke gundumar Guzhang.
Cao Caiyun: A sa kowane digon ruwa ya taka rawar da ta kamata
“Ta yaya za a tabbatar da samar da isashen abinci a kasarmu, da kuma tabbatar da kowane digon ruwa ya taka rawar da ta kamata, abu ne da ke matukar jan hankalina”, in ji Cao Caiyun, ‘yar majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, wadda kuma ma’aikaciya ce a cibiyar nazarin aikin gona mai tsimin ruwa da ke kwalejin nazarin harkokin noma da dazuzzuka na lardin Hebei.”
Lardin Hebei yana arewacin kasar Sin, lardi ne da ake yawan noman hatsi, wanda kuma ke daga cikin yankunan da ke fama da karancin ruwa a kasar Sin. Don haka ma, bunkasa aikin gona mai tsimin ruwa ya kasance muhimmiyar hanya wajen daidaita sabanin da ke tsakanin aikin noma da ruwa. Don haka ma, malama Cao Caiyun da ma sauran abokan aikinta sun mai da hankali a kan nazarin hanyoyin tsimin ruwa ta fannin ayyukan gona.
An shekarar 2023, a matsayinta na sabuwar ‘yar majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da aka zaba, Cao Caiyun ta gabatar da wasu shirye-shirye biyu dangane da bunkasa aikin gona mai tsimin ruwa, bisa nazarin da ta shafe shekara da shekaru tana yi.
Cao Caiyun ta ce, “A kasarmu, ana yawan samun ruwan sama a lokacin zafi, a yayin da ake fuskantar karancin ruwa a lokacin dari. Ban da haka, ana yawan samun ruwa a kudancin kasar, a yayin da ake karancin ruwa a arewaci. Matsalar karancin ruwa tana yi wa wadatar abinci da bunkasuwar ayyukan noma tarnaki, don haka ma, kirkire-kirkiren fasahohi ta fannin aikin gona mai tsimin ruwa na da ma’ana sosai wajen daidaita matsalar.”
Cao Caiyun ta ce, bayan taron shekara shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da aka gudanar a watan Maris na bara, ta samu martani daga sassan da abin ya shafa dangane da shirye-shiryen da ta gabatar, matakin da ya ba ta kwarin gwiwa matuka.
Bayan taron, nan da nan Cao Caiyun ta koma bakin aiki, inda ta fara daukar samfura daga gonaki. Ta ce, “Watan Maris muhimmin lokaci ne da manoma suka fara ban ruwa a karo na farko, kuma lokacin aikin noma na da muhimmanci sosai wajen tattara adadin da muke bukata wajen nazari.”
A matsayinta na ‘yar majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, baya ga aikin nazari, malama Cao Caiyun ta kan kuma ba wa manoma kwarin gwiwar gudanar da ayyukan gona a kimiyyance. Kwalliya ta biya kudin sabulu, a bara, rukunin hadin gwiwar manoma na Liangfeng da ke gundumar Jing ta lardin Hebei, ya cimma nasarar karuwar alkama da masara da aka girba da kaso 15.5% da kaso 16.7%, a yayin da ruwan da ake samar ga gonaki ya ragu, sakamakon hanyoyin ban ruwa na zamani da aka dauka.
Dimokuradiyya hanya ce ta warware matsalolin da al’umma ke fuskanta
Malam Long Xianwen da malama Cao Caiyun na daga cikin ‘yan majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14 da gaba dayansu suka kai kusan 3000, wadanda suke gudanar da aikinsu don bauta wa al’ummar kasar. A kasar Sin, ban da ‘yan majalisar wakilan jama’a a mataki na kasa, akwai kuma ‘yan majalisar wakilan jama’a a matsayin larduna da birane da gundumomi da garuruwa, wadanda suke wakiltar al’umma ‘yan kabilu daban daban da ma mabambantan yankuna da sana’o’i. ‘Yan majalisar a matakai daban daban sun bayyana ra’ayoyin al’umma da sa ido a kan yadda gwamnati ke tafiyar da harkoki da kuma sa kaimi ga warware matsalolin da al’umma ke fuskanta a turbar dimokuradiyyar al’umma baki daya.
A ganin gwamnatin kasar Sin da al’ummarta, dimokuradiyya ba ado ba ne, hanya ce ta warware matsalolin da al’umma ke fuskanta, kuma dimokuradiyya na da mabambantan salo a kasashe daban daban bisa yanayin da suke ciki. Kasancewar kasar Sin kasa mai fadi wadda ke da yawan al’umma a duniya, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta hada gwiwa da sauran jam’iyyun siyasa na kasar, suka gano hanyar dimokuradiyyar da ta dace da yanayin da take ciki.
Jama’ar kasa ne suke da ‘yancin tabbatar da ko kasar na kan tafarkin dimokuradiyya ko a’a. Binciken sauraron ra’ayoyin al’umma ya shaida cewa, cikin ‘yan shekarun baya, gwamnatin kasar Sin ta kiyaye sama da kaso 90% na amincewar da al’ummarta suka nuna mata, lamarin da ya shaida ingancin dimokuradiyya a kasar Sin.