An gudanar da taron tattaunawa tsakanin kafofin watsa labaru na kasa da kasa mai taken “Sin a lokacin bazara” a kasar Amurka a jiya. Babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ne ya dauki bakuncin taron, inda kuma reshen Chicago na kungiyar ‘yan kasuwan kasar Sin dake Amurka ya taimaka wajen gudanar da shi.
Shugaban CMG Shen Haixiong da jakadan Sin dake kasar Amurka Xie Feng sun gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. Mahalarta taron fiye da dari daya daga bangarorin siyasa da kasuwanci da ilmi na kasar Amurka sun yi musayar ra’ayoyi kan batun zuba jari ga kasar Sin da more moriyar bunkasuwa tare.
- Bai Kamata A Yi Amfani Da Ma’auni Biyu Kan Batun Kare Hakkin Dan Adam Ba
- Kasar Sin: Yunkurin Amurka Na Takaita Karfin TikTok Zai Yi Illa Ga Muhallin Zuba Jari Na Kasa Da Kasa
Shen Haixiong ya bayyana cewa, bisa kuri’un jin ra’ayoyin al’umma na kasa da kasa da kafar CGTN ta babban gidan CMG ya gabatar, kashi 93.1 cikin dari sun yi tsammanin cewa, tattalin arzikin Sin yana da karfi da kyakkyawar makoma, kana ya samar da damarmaki da yawa. Ya ce CMG yana mayar da hankali kan kokarin samar da gudummawa wajen sada zumunta da neman hadin gwiwa tsakanin jama’ar Sin da Amurka da sauran sassan duniya.
A nasa bangare, jakada Xie Feng ya bayyana cewa, Sin tana maraba da karin kamfanonin Amurka su zuba jari da aiwatar da ayyuka a kasuwar kasar Sin, kana tana fatan bangarori daban daban za su taka rawa wajen sa kaimi ga yin mu’amala da fahimtar juna a tsakanin Sin da Amurka, da kirkiro kyakkyawar makomar duniya ta hanyar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Amurka. (Zainab Zhang)