5. Samar Da Yanayin Da Zai Kara Wa Malamai Kwarin Gwiwa
Wurin da Malaman makaranta suke aiki ya na bada gudunmawa kwarai wajen bunkasa aikinsu, sai dai kuma idan basu samun lokaci na hutawa ga kuma gajiya, irin hakan ba zai haifar da da mai ido ba domin ba za su samu kwarin gwiwa ba wajen aikinsu.Idan mutum na neman yadda za ka taimakawa Malamai wajen gabatar da aikinsu sai ka fara samar da ko tunanin samar da duk abubuwan da za su taimaka.
Lura da yadda ake tafiyar da aki a makarantar ka.Ka yi sauye- sauye idan kana ganin Malamanka ayyukan da suke yi sun yi masu yawa.Malaman suna kara samun kwarin gwiwa ne idan yadda suke gudanar da ayyukansu ana taimaka masu da abubuwan da za su ja hankalinsu su kara zage – damtse ga aikinsu.Makarantu ko kwaleji sau da yawa Malaman makaranta
6.Ka Tabbata Malaman Da Ke Aiki Karkashinka Ba Su Fuskanatar Matsala Wajen Gudanar Da Aikinsu
Bayan sun yi aiki a makaranta ko kwaleji Malaman makaranta sau da yawa suna korafin cewar basu samun lokacin da za su kasance da ‘ya’yansu da sauran Iyalai, rashin tsara yadda za ayi aiki kan iya sa Malamai su gaji da rashin sha’awar yin aikin kamar yadda ya dace.
Ka lura sosai da irin wannan al’amarin wajen taimaka wa Malaman makarantar ka yadda za su tafiyar da aikinsu da abubuwan da suka shafe su ba tare da daya ya cutar da daya ba.
Ka yi bincike domin ka gano wadannan abubuwan
Wadanne abubuwa ne Malaman makaranta suke fuskanta a wurin aiki?
Wadanne taimako suke bukata domi samun maslahar matsalar?
Shawarwarin da suka bada na iya taimakawa wajen gano bakin zaren.
Da Zarar ka gane yadda matsalolin suke sai ka samar da wasu hanyoyin da kake ganin za su ko na iya taimakawa wajen maganin matsalolin da suke fuskanta.Idan yadda Malaman makaranta ke gudanar da ayyukansu babu wata matsala da kuma samun isasshen lokacin da za su kasance da iyalansu,hakan zai sa su kara maida hankalinsu wajen gudanar da aikinsu cikin farinciki.
Abu daya misalin da zai bada sha’awa shine Duolingo, ita ce hedikwatar a Pittsburgh,Pennsylbania,ba kawai su samu nasara wajen fafutukarta ta bunkasa koyon harshe ta kafofin koyo na zamani.Amma an bada fifiko ko muhimmanci wajen samar da abubuwan da za su jawo hankalin ma’aikata maida hankalinsu wajen gudanar da aiki yadda ya dace.Kamfanin ya lura da amincewa da muhimmancin samar da duk abubuwan da suka dace tsakanin ayyukansu da suka koya a makaranta da lura da iyalansu.
Mai da hankali ko sa ido na yadda za a dudanar da ayyuka kamar dai irin salon Duolingo da suka hada da yadda abubuwan suke a tsarin yadda ake tafiyar da ayyuka da kuma tsare- tsare na Kamfani.Wadannan sun hada da tsare- tsare da za su taimaka wajen samar da awowin yin aiki, ba ma’aikata amfani da tsarin aikin da zai taimaka wajen cimma burinsu ko bukatunsu.
Da ya ke ya gano duk abubuwan da za su yi maganin matsalolin da ma’aikata suke fuskanta da suka hada da abubuwan da ake sa ran ma’aikata za su yi ko ya kamata su yi sai Duolingo shi ma ya bada ta shi gudunmawar yadda kowa zi kasance ya amince da kuma jin dadin shi al’amarin gaba daya.
Bugu da kari kamfanin ya maida hankali kan yadda al’amuran suke kai har ma abin ya zarce yadda ake bukata na nau’oin ayyuka.Duolingo ya maida hanakali yadda ya dace ayi saboda kuwa ya lura da cewar duk wurin aikin da aka samar da abubuwan da za su taimakawa masu gudanar da aikin wajen maida hankalinsu ga yin aikin kamar yadda ya dace, ko shakka babu za a samu cimma buri ta kowane bangare.
7.A Rika Bikin Ranar Haihuwa Da Shekarun Da Aka Yi Aiki
Yin biki na muhimman ranaku na Malamanku hakan zai dauki lokaci mai tsawo wajen bunkasawa Malamai ko kara masu kwarin gwiwa.
Ana iya biki ranar haihuwa, shekarun aiki da duk wani ci gaban da aka samu, kamar aure, ranar Malamai ta duniya da sauransu saboda yin hakan zai sa suma su san an dauke su da muhimmanci.
Bikin wani ci gaba ko wani abu na ma’aikatanka zai sa su gane cewa an dauke su da muhimmanci, hakan zai rika sa su gane cewa suma naka ne.