Ana so mai azum ya yi Buɗa-baki da dabino idan Allah Ya hore masa. Akwai hadisi akan haka;
1. An karɓo hadisi daga Salmanu dan Ãmir Allah Ya ƙara yarda a gare shi, daga Annabi (S.A.W) ya ce: “Idan ɗayanku zai yi Buɗa-baki, to, ya yi da dabino, idan ba shi da shi, to, ya yi da ruwa, domin tabbas ruwa abu ne mai tsarki” hadisi ne mai kyau Dãrimi ne ya ruwaito [#1743].
2. An karbo hadisi daga Anas ɗan Malik Allah Ya ƙara yarda a gare shi, ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana buɗa-baki da nunannen dabino, idan bai samu ba sai ya yi da busasshe, idan bai samu ba sai ya kamfaci ruwa ya sha” Hadisi ne ingantacce Abu Dãwūd ne ya ruwaito [#2356] da Tirmizi [#696] da Ahmad [#12676]
Ana so mai azumi ya yi addu’a a lokacin buɗa-baki, domin addu’arsa karɓaɓɓiya ce. Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Addu’a guda uku ba a ƙin karbarsu, addu’ar mai azumi da ta wanda aka zalunta da kuma ta matafiyi” Tirmizi ne ya ruwaito [#2528] da Ibnu Maja [#1852] da Ibnu Hibbãn [#2407].
An karbo hadisi daga Abdullahi ɗan Amru dan As, Allah Ya ƙara yarda a gare su, ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce:” Mai azumi yana da karbabbiyar addu’a a lokacin buɗa-baki, kuma ba a ƙin karbarta” Ibnu Maja ne ya ruwaito [#1753] al-Imam al-Busiri ya inganta hadisin a Misbãhuz Zujãjati [2/81].