Allah Ta’ãla ya umarci bayinsa muminai da su ciyar daga cikin abin da ya azurta su da shi na dukiya, inda ya ce: “Ya ku muminai ku ciyar daga cikin abin da muka azurta ku da shi” Suratul Bakara aya ta 254.
Ita wannan ciyarwa ana so ne a yi ta da dukiya ta halas. Allah ya ce: “Ya ku muminai! Ku ciyar daga cikin dadadan abin da kuka tsuwurwurta da kuma abin da muka fitar muku da shi daga cikin kasa” Suratu Bakara aya ta 267.
Duk ciyarwar da aka yi da dukiya ta haram, to, Allah ba zai karɓa ba. Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Ya ku mutane! Lalle Allah Mai tsarki ne, ba ya karɓar aiki sai mai tsarki” Muslim ne ya ruwaito [#1015] da Tirmizi [#2989] da Darimi [#2759] da Ahmad [#8348].
Duk abin da bawa zai ciyar, Allah yana sane da shi. Allah ya ce: “Kuma duk abin da kuka ciyar na duk wani nau’in abinci ko abun ciyarwa ko kuka yi bakancensa, to, lalle Allah yana sane da shi” Suratul Bakara, aya ta 270. Allah ya ce: “Kuma duk abun da kuka ciyar na alheri, to, Allah yana sane da shi” Suratul Bakara aya ta 273.