Fadar shugaban kasa ta karyata wani labarin da wasu kafafe suka yada kan cewa hukumar tsaron farin kaya ta (DSS) ta aike wa shugaba Muhammadu Buhari wasikar nusar da shi kan cewa tikitin takarar shugaban kasa da mataimakin na Musulmi da Musulmi da APC ta yi zai iya janyo yamutsi da barazana ga zaman lafiyan kasar nan.
Wata kafar yada labarai ta yanar gizo ‘Peoples Gazette’ ce ta tsegunta labarin tare da cewa babban mashawarcin shugaban kasa kan tsaro Babagana Monguno ne zai yi bayanin rahoton da DSS din suka fitar.
- Gwamnan Gombe Ya Yi Alhinin Rasuwar Sheikh Maigano Da Ya Rasu A Saudiyya
- Jam’iyyar APC Ta Rusa Kungiyoyin Yakin Zaben ‘Yan Takara
Sai dai mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu a sanarwar da ya fitar ranar Juma’a, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da rahoton tare da misalta ta a matsayin abun da dariya da almara.
Ya ce rahoton kawai da aka yada na da nufin janyo rarrabuwa da damuwa kan zabin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa ne.