• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amurka Na Dauke Da Nauyin Dakatar Da Kisan Fararen Hula A Rafah

by CGTN Hausa
2 years ago
Amurka

Yayin da dubban Falasdinawa dake arewacin zirin Gaza ke tserewa zuwa kudanci, sakamakon yakin da sojojin Isra’ila suka kaddamar na murkushe kungiyar Hamas tun daga ranar 7 ga watan Oktoban bara, masharhanta da dama na ganin lokaci na kara kurewa, na kawo karshen wannan tashin hankali, duba da cewa ga alama matakan sojin da Isra’ilan ke dauka ba abu ne da zai kare a nan kusa ba.

Ya zuwa yanzu, hare-haren sojojin Isra’ila sun kora sama da mutune miliyan guda wani lungu dake kudancin Gaza, inda birnin Rafah ya zamo “Gaba kura baya sayaki” ga masu tserewa hare-haren Isra’ila.

  • Xi Jinping Ya Nanata Wajibcin Yin Kwaskwarima Da Kirkire-Kirkire Cikin Hakikanin Hali A Lardin Hunan
  • Majasirdin Sarkin Zazzau, Alhaji Yusuf Saleh Barde Ya Rasu

Duk da jan hankali da aka sha yi masa, firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya dage cewa sai sojojinsa sun kaddamar da hare-hare a Rafah. Alkaluma sun nuna cewa, kafin wannan tashin hankali, Rafah na da kimanin mutane 275,000 ne kacal, amma yanzu mutane sama da miliyan 1.4 ke cunkushe a cikinsa, a yanayi na matukar bukatar jin kai.

Majalissar Dinkin Duniya, da kungiyar tarayyar Turai ta EU, sun nuna damuwa game da mummunan tasirin da hare-hare a Rafah za su yi ga fararen hula. A daya hannun kuma, a baya bayan nan ita ma kasar Sin ta bayyana damuwa, game da yadda rikicin Falasdinu da Isra’ila ya haura watanni 5, kana yanayin jin kai a wurin ke kara tabarbarewa, don haka ta bayyana wajibcin gaggauta tsagaita wuta nan take, da yin iyakacin kokarin kiyaye rayukan fararen hula, da kuma rage matsalolin jin kai.

Mun san dai da fari, Amurka na sahun gaba wajen marawa Isra’ila baya a wannan yaki mai muni, amma a yanzu ta fara sauya matsaya, har ma an jiyo shugaba Joe Biden na Amurkan na cewa, kaiwa birnin Rafah hare-hare zai zama kuskure mai matukar muni.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

La’akari da goyon baya da Amurkan ta nunawa Isra’ila tsawon lokaci kan wannan batu, ta hanyar maimaita dakatar da kudurin kwamitin tsaron MDD game da tsagaita wuta a Gaza, da tarin makamai da ta rika aikewa Isra’ila, da ma yadda kalaman sauya matsayar ta suka fara sanya Isra’ilan nuna alamun sassautawa. Muna iya cewa idan akwai wani karfi da zai iya sauya yanayin da ake ciki a Gaza ba zai wuce Amurka ba. Ko da yake wasu masu sharhi sun ce gwamnatin Amurka mai ci ta fara sauya matsaya ne saboda al’ummunta sun fara bore, inda a baya bayan nan masu zanga-zanga a jihar Michigan, suka rika daga kyallaye masu dauke da sakon “Idan ba a dakatar da wuta ba, ba za a yi zabe ba”.

Koma dai mene ne ke faruwa a siyasar cikin gidan Amurka? Abun da ya fi damun al’ummun duniya masu son zaman lafiya, shi ne fatan ganin Amurka ta yi abun da ya dace, ta saurari ra’ayoyin sauran sassa, ta kuma goyi bayan dakatar da bude wuta a Gaza, da wanzar da zaman lafiya mai dorewa a yankin gabas ta tsakiya baki daya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

November 3, 2025
Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar
Daga Birnin Sin

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik
Daga Birnin Sin

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Next Post
CIYARWA [Falalarta Da Muhimmancinta] Na 1

CIYARWA [Falalarta Da Muhimmancinta] Na 2

LABARAI MASU NASABA

Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

November 3, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

November 3, 2025
Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

November 3, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

November 3, 2025
Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi

Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi

November 3, 2025
Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano

Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano

November 3, 2025
Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT

Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT

November 3, 2025
Sabon Muƙaddashin Shugaban PDP Ya Sha Alwashin Maido Da Martabar Jam’iyyar Kafin 2027

Sabon Muƙaddashin Shugaban PDP Ya Sha Alwashin Maido Da Martabar Jam’iyyar Kafin 2027

November 3, 2025
2023: Gwarazan Jam’iyyu A Karon Battar Zaben Shugaban Kasa

Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso 

November 3, 2025
Likitoci

NARD Ta Yi Fatali Da Iƙirarin Gwamnatin Tarayya Na Ba Ta ₦43bn, Kuma Yajin Aiki Na Nan

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.