A wani yunkuri na inganta tsaron iyakokin Nijeriya da magance kalubalen tsaro a Arewa Maso Gabas, Kodinetan shiyyar C na Hukumar Shige Da Fice ta Kasa (NIS), ACG James Sunday, ya jagoranci wani muhimmin taro a Jos, babban birnin Jihar Filato. Â
Taron ya samu halartar Kwanturololin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Yobe, da kuma Jihar Filato.
- Zulum Ya Rabawa ‘Yan Sa Kai Da Mafarauta 5,523 Naira Miliyan 255 Da Buhunan Shinkafa 5,513
- Majasirdin Sarkin Zazzau, Alhaji Yusuf Saleh Barde Ya Rasu
Shiyya C, kasancewarta daya daga cikin shiyyoyi takwas masu muhimmanci ga hukumar NIS, na taka muhimmiyar rawa a harkokin tsaron kasa, musamman idan aka yi la’akari da matsalolin tsaro da suka addabi yankin Arewa maso Gabas.
ACG James Sunday ya jaddada bukatar karfafa kokarin da ake na ganin an samar da tsaro a iyakokin kasar nan, musamman bisa ga umarnin da Shugaba Tinubu ya bayar na sake bude iyakokin Nijeriya da Nijar.
Bayan taron, an cimma yarjejeniya tsakanin Kwanturololin, na daukar sabbin dabaru da matakan tsaro a kan iyakoki, tare da jaddada hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.
Kazalika, Kodinetan ya nuna muhimmancin hadin kai a tsakanin mataimakin gwamnan Jihar Filato, jami’an gwamnati da hukumomin soji a Jos.
ACG James Sunday ya sake nanata kudurin tabbatar da tsarin ‘Ba sani ba sabo’ a fannin kula da iyaka, kamar yadda mai girma ministan harkokin cikin gida ya bayar da umarni.
Abu mafi jan hankali a taron shi ne taron kam tsaron iyakokin Arewa Maso Gabas da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum zai jagoranta.
Taron wanda aka shirya gudanarwa a Maiduguri, na da nufin hada kan masu ruwa da tsaki, ciki har da masu sarautar gargajiya, domin magance matsalar tsaro gaba daya a yankin.
Domin tabbatar da tsaro da ayyukan hadin gwiwa na kasa, ACG James Sunday da tawagarsa sun jaddada muhimmancin goyon bayan masu ruwa da tsaki a matakai daban-daban don tabbatar da tsaro ga kasa baki daya.