Al’ummar Musulmi a sassa daban- daban na kasar nan sun shigo mako na biyu suna gudanar da azumin watan Ramadan mai albarka a cike da matsanancin kuncin rayuwa a dalilin tsadar rayuwa da galibin jama’a ke Kallon ita ce irin ta ta farko da suka shaida a Nijeriya.
Farashin dukkanin nau’ukan kayan abinci da na sauran abubuwan amfanin yau da kullum sun ninka ninkin ba ninkin wanda hakan ya sa jama’a ke cikin kunci da tsananin matsin da rugujewar tattalin arzikin kasa ya jefa su a ciki.
- Sin Za Ta Inganta Zamanintarwa Bisa Bunkasuwa Mai Inganci Don Ba Da Karin Karfi Ga Ci Gaban Duniya
- Ɗiawara Ya Fice Daga Tawagar Faransa Bayan An Hana ‘Yan Wasa Yin Azumi
Baya ga tsadar rayuwa da ake fuskanta, haka ma jama’a a sassan kasar daban- daban suna kukan tsananin zafin rana da ake fama da shi ba kakkautawa tare da tabarbarewar samun hasken wuta wanda babban kalubale ne ga al’umma musamman a wannan watan mai tsarki.
Al’ummar Musulmi a Nijeriya kusan miliyan 80 ne suka dauki azumin bana da karancin abin da za su ci. Inda ake tunanin miliyoyin magidanta ba su da wata hanya ta samun abincin da za su yi sahur da buda baki face sun dogara ga gwamnati da masu hannu da shuni.
Duk da a lokutan baya an sha gudanar da azumi a cikin matsi, amma cire tallafin man fetur, tashin farashin dala da wasu manufofin gwamnati kan tattalin arzikin kasa sun sa na bana ya sha bambam da saura.
Masu fashin bakin al’amurran yau da kullum da dimbin al’umma da dama sun ta’allaka halin matsin da al’umma suke ciki a dalilin sayar da ‘yancinsu a babban zaben 2023.
A ra’ayoyin mutane da dama da LEADERSHIP Hausa ta tattauna da su, azumin wannan shekarar hakuri ya zama dole domin a birni da karkara masu kuka sun fi masu dariya yawa kamar yadda wasu magidanta suka bayyana.
“Gabanin zuwan azumi muna cikin wani azumi, yanzu niyya kawai muka canza, amma abubuwan sun wuce duk yadda ake tunani sai dai mu dukufa ga yin addu’oi a wannan watan mai albarka kan Allah ya sauwaka ya kawo mana mafita.” In ji Haruna Bodinga.
“Mun ci taliya mun rasa taliyar azumin bana, a yau kwalla a idanun kowa. Ba wai samun kayan marmari ba da duk mai azumi ke bukata ba, a’a su ba a ma maganarsu don abin da za mu ci tuni ya gagare mu, komai ya yi tsadar da ya fi karfin talaka, tuni mun ajiye maganar cin shinkafa sai dai gari da, dawa da masara ko su ba kullum ake samun a ci a koshi ba. “Cewar Sa’idu Mai- Baro.
Hajo Jauro ta bayyana cewar azumin bana ba a cewa komai domin maigidanta ya kwanta dama ya bar mata marayu shida kuma dukkaninsu kanana, ba wanda ke iya nemar wa kansa. “Muna cikin mawuyacin hali, aikin wanke-wanke nake yi domin in samu damar kula da marayun da mijina ya bar mani.
“A yanzu duk inda muka ji a na bayar da sadakar abinci can muke zuwa, ba domin zuciya ta mutu ba sai don ya zama dole. Jiya na samu kwano biyu na shinkafa, haka za mu dafa mu ci da mai da ya ji.” Ta bayyana.
Al’ummar Musulmi da dama wadanda ke aiwatar da ayyukan karfi domin rufa wa kai asiri a jihohi da dama sun fito da wasu hanyoyin saukaka wa kansu a bisa ga tsadar rayuwa, zafin rana da rashin wuta kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Tsalha Abubakar, lebura a Sakkwato karara ya bayyana cewar “A bisa ga dole nake zuwa wajen aikin karfi, saboda an dakatar da albashina saboda ban yi jam’iyyar da ke mulki ba. Yanzu aikin jinga muke yi maimakon wuni kuma abin da ake samu ba ya isa a kula da iyali, illa dai wannan ya zama darasi ga al’ummar kasa bakidaya kan mu daina biye wa son zuciya, domin idan da jama’a, ba su karbi taliya, kudi da sabulu ba, suka daure aka yi zaben kyautata goben mu da yanzu ba wannan zancen muke yi ba.”
Kokarin Gwamnatoci Da Masu Hali Na Ciyar Da Jama’a
A kokarin saukaka wa al’umma a watan Ramadan, gwamnatocin jihohi da dama da masu hannu da shuni suna aiwatar da shirye-shiryen ciyar da jama’a buda baki a cibiyoyin musamman da aka kafa, a yayin da wasu jihohin kuma kan bayar da kayan abincin domin jama’a su sarrafa a gida. Jihohin da dama kama daga Kaduna, Katisina, Kano, Kebbi, Sakkwato da Zamfara da sauransu suna ta aiwatar da mabambantan tsare-tsare na sanyaya wa jama’a a watan mai albarka.
A bana gwamnatin jihar Katsina, a karkashin jagorancin Dikko Umar Radda ta fitar da tsabar kudi naira biliyan 10 domin saye da rarraba wa jama’a abinci a kananan hukumomi 30 da ke a Jihar. Gwamnatin ta ce mutum dubu 72, 200 ne za su amfana da tallafin abincin a kullum, haka ma gwamnan ya saukaka farashin masara, dawa da gero a kan naira dubu 20 a kowane buhu, haka ma za a bai wa tsofaffin magidanta da marsa galihu dubu 33 abinci da kudade.
Ita ma Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kebe naira biliyan 6.7 domin tallafa wa al’umma a watan Ramadan daga ciki har da bayar da rabin alwashin wata kyauta ga ma’aikata. Daga ciki za a ciyar da marasa galihu a cibiyoyin buda baki 605 a fadin jihar. Gwamnan ya ce za a kashe naira biliyan 1.2 a cibiyoyin mazabu, a yayin da za a kashe naira milyan 797 a cibiyoyi 335 da dama ake da su.
Haka zalika, Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya kaddamar da rabon abinci kyauta ga al’ummar Musulmi akalla 10,000 a Jihar Kano, jiharsa ta asali, ta hannun Gidauniyarsa.
Har ila yau, gidauniyar ta fadada karamcin ta hanyar raba buhunan shinkafa miliyan daya da kudinsu ya haura Naira biliyan 13 a fadin jihohi 36 na tarayya da Babban Birnin Tarayya Abuja domin rage yunwa a kasar nan.
Wannan duka kari ne a kan rabon burodi 20,000 a kullum ga mazauna Kano da kuma wasu 15,000 ga mazauna Legas, inda tsarin ciyarwar da aka fara kuma ya dore tun daga 2020 a lokacin annobar COBID-19.
Abincin da ake dafawa na buda-bakin Ramadan kyauta ya hada da shinkafa dafa-duka, farar shinkafa da miya, taliya dafa-duka, doya, wake da naman kaza da na saniya, kana da ruwan sha na gora ga kowane mutum.
Ana raba kunshin abincin ne a masallatan Juma’a da tituna da gidajen yari da gidajen marayu da gidajen riman (na tsare mutane) da sauran wurare a cikin birnin Kano da kewaye.
Wani da ya ci gajiyar abincin mai suna Musa Maikatako, mazaunin Tarauni ya nuna jin dadinsa da wannan karimcin wanda ya ce ya taimaka masa wajen yin buda baki cikin sauki.
Maikatako, wanda a bayyane fuskarsa na cike da farin ciki, ya ce abinci na kyauta ya kawar da wahalhalun da jama’a da dama za su iya fusktan wajen yin buda baki da ruwa kawai, ba tare da abinci ba, bisa la’akari da halin kuncin da ‘yan Nijeriya ke ciki.
“Ba zan iya bayyana irin farin cikin da nake ciki ba, wannan abincin zai taimaka matuka wajen taimaka wa talakawa kamar ni mu samu abin da za mu yi buda baki da abinci mai nauyi.
“Na san mutane da yawa a jihar nan wadanda za su iya yin buda baki da ruwa kawai. Don haka wannan abincin ya kawo sauki kwarai da gaske,” in ji shi.
Har ila yau, wata da ta ci gajiyar tallafin, Hajiya Inna Tukur, ta bayyana jin dadin ta da rabon abincin, “A cikin wahalhalun da ake fama wanda yana da kamar wuya mu iya cin abinci ko da sau biyu a rana, amma sai ga shi cikin ludufi, an samu wani yana taimaka mana da abinci mai lagwada, gaskiya wannan ba karamin abu ba ne.” In ji ta.
A bisa ga halin da ‘yan kasa suke ciki, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewar suna cikin zuciyar Shugaba Tinubu kuma suna iyakar kokari domin ganin an fita daga kangin da ake ciki.
Ya bayyana cewar ba za su taba yin kasa a guiwa ba sai sun tabbatar al’amurra sun daidaita. Mataimakin Shugaban Kasa ya bayyana hakan ne a wajen taron kaddamar da littafi kan rayuwar Shugaba Tinubu a ranar Talata a Abuja.
Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana wajibcin da ke akwai na masu hannu da shuni da su kara azamar taimakawa mabukata domin saukaka masu halin kuncin da suke ciki na kasa iya rike iyalansu.
“Ramadan din bana ya zo da kunchi na talauci kwarai a gaske, wadanda a shekarun baya sun fi karfin abin da za su ci, bana ya fi karfin su, wadanda a bara suke taimakawa wasu a bana sai an taimake su, kuma wallahi da yawa daga cikin al’umma haka ake.” A cewar Malamin a tafsirinsa na farko a wannan watan.
Malamin, tsohon Ministan Sadarwa ya kara da cewar “Mu gane cewa abin da muka ciyar shi ne namu, wanda muka rike ba namu ba ne, bayin Allah na kwarai sukan iya cin bashin abin da bai fi karfin su ba domin su ciyar da mabukata saboda Allah, wajibi ne abin da muke yi ya karu, idan da ina ciyar da mutum 10 kafin Ramadan, to a Ramadan din ya kai mutum 30.”
Ana Sa Ran Al’amura Su Yi Sauki Bayan Bude Iyakokin Nijeriya Da Nijar
Matakin da Gwamnatin Nijeriya ta dauka a makon jiya na bude bakin iyakokin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar ta sama da kasa ba tare da bata lokaci ba ya sanya farin ciki a zukatan al’ummar kasashen biyu makwabtan juna.
Sanarwar bude bakin iyakokin wadda Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayar da umurni a ranar Larabar makon jiya ta kuma bayyana dage takunkumin huldar tattalin arziki da aka kakaba wa Nijar da wasu kasashen da aka yi juyin mulki.
Tun da farko Nijeriya ta rufe bakin iyakokinta na sama da kasa da Jamhuriyar Nijar a sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar a watan Yuli da yanke wutar lantarki da Nijeriya ke bai wa kasar. Haka ma kungiyar kasashen ECOWAS ta sanya takunkumin dakatar da huldar kasuwanci da hana zriga-zirga ta sama ga dukkanin jiragen kasuwanci a Nijar.
Tuni dai a ranar ta Laraba aka mayar da wuta a Nijar a bisa ga umurnin na Shugaban Kasa wadda aka yanke a ranar 3 ga Augusta wanda sakamakon tsinkewar al’ummar kasar sun kara shiga cikin kunci.
Umurnin Shugaban Kasa ya biyo bayan amincewa da sakamakon zaman tattaunawar shugabannin kungiyar kasashen ECOWAS a ranar 24 ga Fabrairu a inda suka aminta da dage takunkumin da suka Sanya wa kasashen Nijar, Mali, Burkina Faso da Guinea.
Al’ummar Nijeriya sun kaasance cikin murna da jin dadin bude bakin iyakar wanda ake da tabbacin al’amuran da suka ta’azzara a dalilin rufewar za su yi sauki, halin kuncin da jama’a suke ciki musamman a wannan azumin na Ramadan zai saukaka musamman ta hanyar samun saukin farashin kayan abinci.
Ana kyautata tsammanin daga takunkumin zai kawo karshen nunin juna da yatsa tsakanin kasashen biyu tare da inganta harkokin kasuwanci da ya tsaya cak tare da bunkasa tattalin arziki da kuma kara wanzar da zaman lafiya da fahimtar juna.
Daya daga cikin mazauna Illela wato bakin iyakar Nijeriya da Nijar wadda jami’an Kwastam suka bude a ranar Alhamis kwana daya bayan sanarwar, wato Garba Ambarura ya bayyana cewar sun kasance cikin murna kamar ranar Sallah a dalilin bude iyakar.
Ya ce ba za su iya fasalta farin cikin da suka yi na daga takunkumin ba, domin tsananin matsi da wahalar da al’ummarsu suka sha ba zai misaltu ba. Ya ce fatarsu wannan zai zama darasi ga mahukunta a Nijeriya domin a cewarsa babu wata riba da aka ci a dalilin takunkumin illa bakar wahala.
Jim kadan bayan rufe bakin iyakokin Nijeriya da Nijar, kayan abinci da sauran kayan masurufi suka yi tashin gwauron zabo tun gabanin farashin dala ya kai yadda yake a yanzu wanda tun farko jama’a da masu fashin bakin lamurran yau da kullum sun bayyana cewar rufe bakin iyakokin zai haifar da gagarumar matsalar hauhawar farashin abinci wanda a yanzu da gwamnati ta cire wannan takunkumin a na kyautata tsammanin nan da dan lokaci kadan al’amurra za su yi sauki sosai duk da cewa har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, Gwamnatin Nijar ba ta saki jiki ta bude iyakokinta ba.
Karuwar Ta’addanci
Baya ga tsadar rayuwa da fadi-tashin dawainiyar azumi, a sassan kasa da dama musamman a Arewa a na ci gaba da fuskantar ayyukan ta’addanci tare da daukar rayukan wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.
An shiga Ramadan din bana da karuwar ayyukan ta’addanci a Arewacin kasar duk da hobbasar kwazon da hukumomin tsaro ke yi ba dare ba rana, amma hare- haren kisan gilla da garkuwa da mutane na ci- gaba da faruwa wanda hakan ya zamarwa al’umma matsala goma da goma, ga tashin hankali ga kuma tsadar rayuwa.
A yanzu haka a na ci gaba da kaduwar satar daliban furamare 287 da ke Kuriga a Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna wadanda iyayen su suna gudanar da azumin bana a cikin kuncin satar ‘ya’yansu wanda har yau ba a ji ko dalibi daya da jami’an tsaro suka samu cetowa ba. A ranar 1 ga Ramadan ‘yan ta’addan sun sake sace mutum 61 a Kajuru da ke Kaduna.
Abin bai tsaya nan ba, a farkon makon nan kuma an sake sace mutum 86 a yankin Kajuru Station baya ga 14 da aka sace a Dogon Noma, tsakanin sa’o’I 24 duka a yankin karamar hukumar ta Kajuru, lamarin da ya kara sanya tsoro a zukatan al’umma.
Haka ma a Jihar Sakkwato, ‘yan ta’addan suna ci gaba da cin karensu ba babbaka, hasalima kwana daya kafin azumi bata garin sun kai hari tare da sace daliban wata makarantar tsangaya 15 da wata mace daya a Gidan Bakuso a Karamar Hukumar Gada.
Sabon Salon Kai Hari Lokacin Buda-baki
Wani abu da ya kara dugunzuma al’umma kuma shi ne wani sabon salon kai hari da ‘yan ta’addan suka bullo da shi yayin da jama’a suke buda-bakin azumi.
Rahotanni sun bayyana yadda ‘yan bindiga suka kai hari a garin Baure da ke karamar hukumar Gusau a Jihar Zamfara da yammacin ranar Talata, lokacin da mutane ke hada-hadar yin buda-baki.
Wani mazaunin garin da BBC Hausa ta zanta da shi, aka sakaya sunansa, ya ce suna zaune da yammacin Talata sai aka fara cewa ga barayi nan sun shigo, nan take kuma suka fara harbi kan mai uwa da wabi.
”Da suka fara harbe-harben mun rasa mafita, sai makwabtanmu suka kawo mana dauki, a nan dai suka kashe mutum biyu da jikkata wasu biyar. Cikin wadanda suka kashe akwai Aliyu Abubakar daga gidan Zuma, sai kuma Barkono Musa daga Suto ta kasar Kwatarkwashi, sauran biyar kuma suna kwance a asibiti,” in ji mutumin.
Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun zo a kan babura 30 dauke da muggan makamai, haka sukayi ta barin wuta a ciki da wajen gidaje.
Wani shi ma da ya shaida abin da ya faru, ya ce da fari a kan babura biyu suka shiga garin na Ruwan Baure, suka tambayi wadanda suka samu zaune ina nasu kason na tallafin da aka bai wa mutanen garin. ”Mun dauka su biyu ne kadai sai muka bi su da gudu, ashe sun yi mana kwantan bauna, sai ganinsu muka yi babura talatin suka fara harbin kan mai tsausayi, suka kewaye garin, haka suka kashe mutum biyu da azumi a bakinsu, bayan wadanda suka raunata da ke samun kulawa a asibiti. Iyalan wadanda suka kashe na cikin mawuyacin hali, saboda hatta abin da za su ci d akyar ake samunsa.
“Mutane sun rinka yanke jiki suna suma saboda gigicewa da dimauta kan halin da suka samu kansu a ciki.” In ji shi.