ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matsalar Tsaro A Nijeriya: Akwai Bukatar Daukar Kwakkwaran Mataki

by Leadership Hausa
2 years ago
Tsaro

Nijeriya ta sake samun kanta a cikin halin tashin hankali, tsoro da alhini, a yayin da rahotanni suke nuna cewa, ‘yan ta’adda dauke da muggan makamai sun yi awon gaba da daruruwan dalibai ‘yan makaranta a wasu jihohin kasar nan, wannan  shi ya dawo da hannun agogo baya a kokarin da gwamnatoci a dukkan matakai suke yi na samar da tsaro a kasar nan.

A kwanakin baya ne ‘yan ta’adda suka sace dalibai 280 da Malaman su daga makarantar LEA da ke garin Kuriga, karamar Hukumar Birnin gwari ta Jihar Kaduna.

  • Ɗiawara Ya Fice Daga Tawagar Faransa Bayan An Hana ‘Yan Wasa Yin Azumi
  • Sin Za Ta Inganta Zamanintarwa Bisa Bunkasuwa Mai Inganci Don Ba Da Karin Karfi Ga Ci Gaban Duniya

Haka kuma wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai hari a yankin Buda da ke karamar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna inda suka yi nasarar sace mutum 61.

ADVERTISEMENT

Duk a ‘yan kwanakin nan, sai gashi kuma ‘yan ta’addar Boko Haram sun yi awon gaba da mata 200 a yankin Gamboru-Ngala da ke karamar hukumar Dikwa ta Jihar Borno.

Rahotannin sun nuna cewa, matan da aka sace na daga cikin ‘yan gudun hijira ne da ayyukan ‘ta’addanci ya raba su da muhallansu a yankin Arewa maso gabas, an kuma sace su ne a yayin da suka shiga daji don neman itacen dafa abinci.

LABARAI MASU NASABA

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Har ila yau mun samu rahoton kashe mutum 50 ciki har da iyalai 7 a harin da ‘yan ta’addan suka kai yankin Gbagir da ke karamar hukumar Ukum ta Jihar Benuwai.

A daidai lokacin da ‘yan ta’addar ke cin karensu babu babbaka sai kuma gashi sun kai hari  a kauyen Gidan Bakuso da ke karamar hukumar Gada can Jihar Sakkwato, inda can ma suka yi awon gaba da almajirai ‘yan makarantar tsangaya 15 wasu kuma da dama ba a samu labara inda suke ba har zuwa yanzu.

A ra’ayin wannan jarida, wadannan ayyuykan ta’addanci ba abin da ya kamata a kawar da kai ba ne; wadannan sun kasance wasu sabbin babi a cikin ayyukan ta’addanci da ya addabi sassan Nijeriya a cikin ‘yan shekarun nan.

Nijeriya ta dade tana dandana kudarta a hannun ‘yan ta’addr  da suke harkokinsu ba tare da wani tsoro ba a sassan Nijeriya.

Wadannan ayyukan garkuwa da mutane da suka sake kunnu kai sun matukar tayar da hankulan al’umma, wadanda suka dade suna sauraron alkawurran masu tafi da kasa na cewa, lallai za a samar masu da tsaro amma kuma har yanzu babu ranar tabbatar da cika wannan alkawarin.

A ra’ayinmu, lokaci ya yi da za a sauya salon da ake amfani da shi a yaki da ta’addanci a Nijeriya. Duk da cewa, gwamnatin Shugaba Bola  Ahmed Tinubu ta gaji wasu daga cikin matsalolin tsaron da ake fuskanta, matsalar da take barazana da kokarin jawo masu zuba jari daga cikin Nijeriya da kuma kasashen waje.

A ra’ayinmu, duk irin abubuwan da Shugaba Tinubu ya shirya gabatarwa na ci gaban kasa, batun samar da tsaro shi ya kamata ya zama a kan sahun gaba don da shi ne tattalin arziki zai karu, musamman ma la’akarin yadda ya tafiyar da tsaro da zaman lafiyar al’ummar kasa, musamman ganin yadda ake kashe mutane da tare da kakkautawa ba.

Matsayar shugaban kasa na kin biyan kudin fansa ga ‘yan ta’adda wannan ma abin a yaba ne. Hakan ya yi daidai da yadda ake tafiyar da irin wannan matsalar a sauran sassan duniya, yana kuma aikawa da sako mai karfi ga su ‘yan ta’addar da ‘yan bindiga na cewa, gwamnati a shirye take da ta murkushe su.

Amma kuma dole gwamnati ta fito da tsari na musamman kan yadda za ta karya alkadarin ‘yan ta’addar ba tare da bata lokaci ba.

Tattaunawa da ‘yan ta’adda da kuma ‘yan bindiga ba zai haifar da da mai ido ba, irin tattaunawar tana kara karfafa kungiyoyin ne kawai da kuma nuna tamkar gwamnati bata da yadda za ta yi.

Muna kara jaddada cewa, bai kamata Nijeriya ta nuna gazawa ba a fafatawarta da ‘yan ta’addar da suka gallaza wa al’umma ba tare da tausaya masu ba. Lokacin da duk wata tattuanawa ta wuce, abin da ake bukata a halin yanzu shi ne fafatawa da gungun masu aikata laifi.

Domin samun wannan nasarar, dole ne Shugaba Tinubu ya karfafa jami’an tsaronmu ta hanyar samar masu da dukkan kayan aiki na zamani daidai da irin wadanda ake amfani da su a kasashe duniya wadanda suka ci gaba.Hakanan kuma a kwai bukatar a karfafa hanyoyin samar da bayanan sirri domin dakile ayyukan ‘yan ta’adda a daidai lokacin da suke shiryawa.

Hakanan kuma ya kamata a yi maganin ainihin  su matsaloli da dalilan da suke taimakawa wajen bunkasar harkokin ta’addanci a Nijeriya wadanda suka hada da talauci, rashin aikin yi ga matasanmu da kuma yadda ake nunawa wasu al’umma wariya a harkokinsu na yau da kullum na kasa.

Ya kamata a samar da ingantaccen tsarin yaki da ta’addanci wanda ya hada da samar da ayyukan bunkasa rayuwar al’umma da suka hada da samar da aikin yi ga matasa, bunkasa bangaren ilimi, kiwon lafiya, da kuma sauraron koke-koken al’umma.

Tsaro
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Yadda Arsenal Ta Lashe Gasar Firimiya Bayan Shekara 22
  • Leadership Hausa
    Bukatar Kawo Karshen Akidar Kyamar Baki A Kasar Afirka Ta Kudu
  • Leadership Hausa
    Ikirarin Cewa Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar, Marafan Sokoto, Nauyi Ne Ga Jihar Zamfara Da Jam’iyyar APC Ba Ta Da Tushe
  • Leadership Hausa
    Nazarin Kisan Gillar Da ‘Yan Kato Da Gora Suka Yi Wa Wani Matashi A Biniwe

MASU ALAKA

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili
Manyan Labarai

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro
Manyan Labarai

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya
Manyan Labarai

Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

June 3, 2026
Next Post
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.