A daidai lokacin da gwamnatin tarayya ta shirya ci gaba da aikin tashar jirgin ruwa na Baro, mazauna yankin sun daura laifin tafiyar hawainiya da aikin kan shirin da aka yi a baya, wanda a cewarsu suna fata sabon tsarin da aka yi kar ya bi sahun tsohon shirin wanda bai kai su ga gaci ba.
Shugaban kungiyar matasan al’ummar garin Baro da ke garin Agaie ta Jihar Neja, Hon Jibrin Ndagi Akwanu ya bayyana wa LEADERSHIP cewa matsalar ba wai kawo kayayyaki aikin ba ne, a tabbatar da cewa tashar jirgin ruwan ta fara aiki kamar yadda hanyoyin ruwa suke aiki.
- Ɗiawara Ya Fice Daga Tawagar Faransa Bayan An Hana ‘Yan Wasa Yin Azumi
- An Fara Taron Kasa Da Kasa Kan Tsarin Dimokuradiyya Karo Na Uku A Nan Birnin Beijing
A cewarsa, gaba daya an dauka cewa an kammala wannan aikin tashar jirgin ruwa ta Baro, amma a batun gaskiya babu abun da aka yi a aikin. Ya kamata masana su bai wa gwamnati shawarar da ake bukata wajen sake yashe hanyar ruwa mu-samman daga Baro zuwa Lakwaja.
“Sabon salon da za a bi shi ne, a bude wasu hanyoyin ruwan ba wai ainihin hanyar da ruwan ke bi ba a baya wadanda suke da zurfi,” in ji shi.
Akwanu ya kara da cewa ya zama wajibi a rika bibiyan aikin tare da sanya idanu a kan tashar jirgin ruwa na Baro wanda baya bukatar wani gyara a yanzu, amma abun da wajen ke bukata shi ne samar da wasu gine-gine masu muhimmanci kamar yashe kogi da hanayar motoci daga Baro.
Ya ce, “Ya zama wajibi a yashe kogin Neja tun daga Baro zuwa Lakwaja, daga Onitsha zuwa Burutu har ya dangana ga Fatakwai kanfi a cewa tashar na Baro ya fara aiki yadda ya kamata.”
Haka kuma ya ce hanyar da ta tashi daga Agaie zuwa Katcha ya sake dawo Agaie ya zama wajibi a gyara a kuma mai da su hanyoyin su koma hannu biyu ta yadda za su hade da Babban Birnin Tarayya Abuja.