Tarayyar Najeriya ta dade tana fama da matsalolin hauhawar farashin kayayyaki, da rashin aikin yi, da talauci, sai dai tambaya a nan ita ce ko ta yaya za a iya daidaita wadannan matsaloli? Jiya na karanta wani bayani da tsohon mataimakin shugaban babban bankin kasar CBN mista Kingsley Moghalu ya rubuta, inda ya gabatar da shawarar daukar wasu matakan kudi masu yakini, da gudanar da mabambantan ayyukan raya kasa. Ban da haka, Mista Moghalu ya ce kafin a iya raya tattalin arzikin Najeriya, dole ne a daidaita matsalar rashin daidaitaccen tunani, da ilimi, masu alaka da tafiyar da tattalin arziki, wadanda a ganinsa ke haddasa rashin daidaito tsakanin matakan gwamnati, da yadda ake kula da al’amura bisa bukatar kasuwa.
Maganar Mista Moghalu ta yi daidai, saboda ba za a iya raba dorewar ci gaban tattalin arziki, da nagartaccen tunani, da ilimi na raya kasa ba. Sai dai ko ta yaya ake iya samun wannan irin tunani ko ilimi? Ko shakka ba bu sai ta hanyar yin musayar ra’ayi. A kwanan baya, yayin taro na 13 na dandalin masana na Sin da Afirka, wanda ya gudana a Dar es Salaam na kasar Tanzania, an gabatar da takardar nuna ra’ayi daya da aka cimma dangane da aikin zurfafa hadin gwiwa a fannin raya kasa. A cikin wannan takardar, an jaddada wasu tunani masu muhimmanci, da suka hada da dogaro kan al’adun kai, yayin da ake neman tabbatar da turbar raya kasa, da mai da moriyar jama’a a gaban sauran batutuwa, da hada karfin matakan gwamnati da na niyyar ‘yan kasuwa, da samar da tsarin kasancewar mabambantan bangarori masu fada a ji a duniya, da dunkulewar tattalin arzikin duniya dake amfanin kowa, da dai sauransu.
- Hukumar NEMA Ta Raba Kayan Abincin Da Kungiyar Bada Agaji Ta Saudiyya Ta Bayar Ga Gidaje 2,056 A Kano
- Kasar Sin Na Maraba Da Abokai ‘Yan Kasuwa Daga Kasashe Daban Daban Da Su Ci Gaba Da Zuba Jari A Kasar
Tunanin da aka gabatar suna da daraja, saboda an same su ne daga cikin fasahohin da kasashen Afirka da kasar Sin suka samu a kokarin raya tattalin arzikinsu, da hadin gwiwar da suke, kana sun fi tunanin da kasashen yamma suka samar cancantar yanayin da kasashe masu tasowa suke ciki.
Kasashen Afirka sun taba amincewa da tunanin raya kasa da kasashen yamma suka gabatar, da gudanar da gyare-gyare bisa tunanin hakan, sai dai sakamakon da aka samu sun nuna cewa, tunanin bai dace da yanayin da suke ciki ba. Misali, kasar Amurka da wasu kasashen Turai sun yi kokarin sanya kasashen Afirka gudanar da kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki, bisa tunani na “Neoliberalism”, matakin da ya kunshi bangaorin “mai da dukiyar kasa karkashin mallakar daidaikon mutane”, da “dogaro kan kasuwa maimakon matakan gwamnati”, da “baiwa kasuwar hada-hadar kudi cikakken ‘yancin gudanar da harkokinta”, da dai sauransu. Sai dai wannan mataki ya dade yana haifar da illa ga tattalin arzikin kasashen Afirka, wanda ya sanya yawan bashin da ake bin kasashen dake kudu da hamadar Sahara karuwa daga dalar Amurka biliyan 2 a shekarar 1970, zuwa dala biliyan 331 a shekarar 2012.
Za mu iya duba misalin kasar Masar, wadda a bisa tunanin raya kasa na “Neoliberalism”, take neman sayar da hannayen jari na kamfanonin gwamnati har 35 a shekarun nan, don neman samun dala biliyan 5, tare da neman rance har dala biliyan 3 daga hukumar ba da lamuni ta duniya IMF. Sai dai wannan mataki na gaggauta sayar da dukiyoyin gwamnati ga daidaikon mutane bai sa kasar samun biyan bukatar raya tattalin arziki ba, maimakon haka, ya jefa kasar cikin mawuyacin hali na fama da hauhawar farashin kayayyaki, da karancin kudin musaya, da matsalar cin bashi fiye da kima. An ce yawan hauhawar farashin kayayyaki a kasar ya riga ya kai kashi 35.7%.
A sauran kasashen Afirka ma, muna iya ganin abubuwan da suka yi kama da batun da ya faru a kasar Masar. Misali, a Najeriya, yadda ake kokarin mai da kamfanonin samar da wutar lantarki karkashin mallakar daidaikon mutane bai saukaka matsalar karancin wutar lantarki a kasar ba.
Sa’an nan a nata bangare, kasar Sin ta kiyaye wani yanayin ci gaban tattalin arzikinta mai sauri, cikin shekaru fiye da 40 da suka wuce. Kana wani babban dalilin da ya sa hakan ya wakana shi ne, yadda kasar ta zabi wata turbar raya kasa da ta dace da yanayin da take ciki, wato tsarin siyasa na gurguzu mai salon musamman na kasar Sin. Ta wannan tsari, kasar ta iya sa kaimi ga ci gaban tattalin arziki, ta kamfanoni masu zaman kansu da harkokin kasuwa, yayin da a lokaci guda, kamfanonin kasar mallakar gwamnati, da matakan zuba jari da gwamnati ta dauka suna tabbatar da yanayi mai karko da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Hakika tun bayan aukuwar matsalar tattalin arziki a duniya a shekarar 2008, tattalin arzikin kasashe masu sukuni bai farfado yadda suke bukata ba. Ko a kasar Amurka, wadda ta fi saurin farfadowa a cikinsu, matsakaiciyar karuwar tattalin arzikinta tsakanin shekarar 2008 da ta 2022 ta tsaya ne a kashi 1.8% kacal. Sai dai a nata bangare, kasar Sin ta kiyaye yanayin ci gaban tattalin arzikinta mai sauri, ta hanyar wasu matakan da gwamnatin kasar ta dauka.
Idan mun yi bitar yadda gwamnatin kasar Sin ke zuba jari da raya kayayyakin more rayuwa, za mu ga tun daga shekarar 2008 zuwa ta 2022, tsawon tagwayen hanyoyi da kasar ta gina ya karu daga kilomita dubu 60 zuwa kilomita dubu 177, yayin da tsawon layin dogon da kasar ta gina wa jiragen kasa masu matukar saurin gudu, ya karu daga kilomita fiye da dubu 1 a shekarar 2008, zuwa fiye da kilomita dubu 45 a yanzu. Wadannan ayyukan gini sun haifar da riba ga dukkan kamfanonin gwamnati, da masu zaman kansu, da samar da gudunmowa ga karuwar tattalin arzikin Sin, wanda ya kiyaye wata karuwa da matsakaicinta ya kai fiye da kashi 6%, tsakanin shekarar 2013 da ta 2022.
Saboda haka, tattalin arzikin Sin ba wani abu da sauran kasashe ke iya gurguntawa ba ne ta hanyar shafa masa bakin fenti. Za a iya duba taron dandalin ci gaban kasar Sin da ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin a kwanan nan, inda wasu shugabannin manyan kamfanonin kasa da kasa kusan 100 suka samu halartar taron. Wadannan mutane sun fahimci jajircewar tattalin arzikin Sin, da dalilin da ya tabbatar da hakan.
Sai dai, ko da yake wani tsarin raya tattalin arziki na iya yin amfani a wata kasa, amma ya ki dacewa da wani wurin kai tsaye, abun da ya fi muhimmanci shi ne a yi kokarin lalubo dabara mafi dacewa da yanayin da ake ciki.
Sa’an nan takardar da aka gabatar a wajen taron dandalin masanan Sin da Afirka, ta nuna dabarar zabar turbar da za a bi, wato a dogara kan tarihi da al’adu na kai, da la’akari da yanayin da wata kasa ke ciki, da zurfafa hadin gwiwar dake amfanar juna, gami da mai da moriyar jama’a gaban komai, inda ake kokarin ba da taimako ga duk wani dan kasa, don ya samu biyan bukatar kyautata zaman rayuwa. (Bello Wang)