Shugaban kasar Nauru David Adeang ya kawo ziyara kasar Sin daga ranar 24 zuwa 29 ga wata. Wannan ne karo na farko da shugaban kasar Nauru ya ziyarci kasar Sin bayan kulla huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu a watan Janairun bana.
Daga maido da huldar diflomasiyya a watan Janairu zuwa ziyartar kasar Sin a watan Maris, manufar Sin daya tak ita ce ginshikin ci gaban dangantakar dake tsakanin Sin da Nauru, kuma a yayin ziyarar shugaba Adeang a kasar Sin, bangarorin biyu sun sake tabbatar da wannan manufa. Ba kawai kiran maido da huldar diflomasiyya da kasar Sin a matsayin “tsayawa a gefen dama na tarihi” shugaba Adeang ya yi ba, har ma da bayyana cewa, wannan wata muhimmiyar alama ta dangantakar kasar Nauru da kasar Sin. Wannan kuma ya sake nuna cewa, manufar Sin daya tak da aka tabbatar a kuduri mai lamba 2758 na babban zauren taron shekarar 1971, ya zama ra’ayin bai daya na duniya baki daya.
- Muna Sane Nijeriya Ta Tsare Ɗan Kasarmu Ma’aikacin Binance – Amurka
- Muna Sane Nijeriya Ta Tsare Ɗan Kasarmu Ma’aikacin Binance – Amurka
A yayin ziyarar shugaba Adeang a kasar Sin, Nauru ta zama wata kasa ta daban da ta rattaba hannu kan takardun hadin gwiwa da Sin don raya shawarar “Ziri daya da hanya daya”.
Manazarta sun yi nuni da cewa, raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” ta inganta matakan tattalin arziki da jin dadin jama’a na kasashe da dama a yankin tekun Pasific. Bisa ga aiwatar da shawarar “Ziri daya da hanya daya” da kasar Sin ke yi tare da hadin gwiwar kasar Nauru, bangarorin biyu suna da burika da yawa na bai daya a fannoni da dama, ciki har da kawar da gishiri daga ruwan teku, da samar da makamashi masu tsabta, da neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da dai sauransu, kuma hakan zai kawo wani sabon kuzari ga zurfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)